Kashe Hauwa Leman Ba Karamin Zalunci Bane –Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da kisan gillar da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka yi ma Hauwa Leman, ma’aikaciyar hukumar “Red Cross” ta duniya.

A jiya Litinin ne, wani bangare na kungiyar Boko Haram mai suna ‘ISWAP’ ya kashe Hauwa Leman din, bayan wa’adin da suka baiwa gwamnatin Nijeriya ya kare, kafin su kashe Hauwan, sun kashe wata abokiyar aikinta mai suna Saifura Khorsa makonni uku da suka gabata.

A cikin sanarwar da Atikun ya fitar daga ofishin yakin neman zaben shi dake Abuja, Atikun ya ce wannan kisan ba karamin rashin imani bane, kuma wannan laifi ne da aka aikata shi ga duniyar dan adam.

Atikun ya tabbatar wa da iyayen Hauwa da na Saifura, zai yi duk yadda zai iya don ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aikin, ba ga iyayensu ba kadai, har da sauran jama’ar kasar nan gaba daya.

‘Duk da munsan babu yadda za ayi ta dawo, amma muna tabbatar wa duk iyalai da ake zalunta ba gaira ba dalili, da wadanda aka kashe musu ‘yan uwa haka siddan, zamu yi duk abinda zamu iya wajen tabbatar musu da adalci, za mu hada hannu da sauran kasashen duniya wajen ganin an kwato sauran mutanen da suke hannun ‘yan ta’adda.’ Inji Atiku.

Exit mobile version