Bello Hamza" />

Kashe-Kashen Taraba: Sojoji Na Neman Mutum Biyar Ruwa A Jallo

A ranar Larabar nan ne rundunar sojojin Nijeriya ta aiyana neman mutum 5 ruwa a jallo dangane da hannun da suke dashi a kashe kashen daya auku a karamar hukumar Takum dama sauran sassan jihar Taraba baki daya.

Wadanda ake neman sun hada da Tanko Adiku Dantayi da Kurusi Danladi da Chindo da Big Olumba da kuma Chairman Poko.

Jami’in wasta labaran rundunar sojojin Brigadia Janar Tedas Chukwu ne ya bayyana haka a wata sanarwa daya saw a hanunn, ya kuma bukaci al’ummar jihar das u mika duk wani bayanin da zai taimaka wa jami’an wajen cafke mutanen ga hukumar tsaro mafi kusa dasu.

Kanfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, rundunar sojojin Nijeriya ta sanar da mutum 2 da suka kissa kashe kashen da aka yi a kananan hukumomin Takum da Ussa ta jihar Taraban. Wadanda aka kama sun hada da Mista Danjuma da Mista Danasebe Gasama.

Jami’in wasta labaran. Brigadia Janar Chukwu, Danjuma, ya ce, an kama wanda a kan kira da suna American da Gasama ne ranar Jumma’a a yayin da jami’an sojoji na rundunar “Operation Ayem Akpatuma” ke sintiri a yankin Takum, bayan da suka samu bayanan asiri na maboyaer mutanen. Ya kara da cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna wadannan mutanen a matsayin wadanda suka jagoranci ta’addancin da aka yi a kananan hukumomin biyu.

Exit mobile version