• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kayan Makulashen Hausawa Na Zamani

by Bilkisu Tijjani
3 years ago
Zamani

Akwai rukuni na abincin Hausawa wadanda su Hausawan ne suke yi ba tare da sun gani daga wata al’umma ba, sai dai kawai don ci gaban zamani ne ya haifar da samuwarsu.

Idan aka kula za a gani wasu daga cikin kayayyakin hadin su ba na gargajiya ba ne na zamani ne, amma za mu fahinci sun yi amfani da basirarsu ta zamani ne suka kirkiro su, kamar yadda aka samu na garajiya. Ga dai kamar haka;

  • Alkawurana Ga ‘Yan Nijeriya Kan Tsaro, Zaman Kashe Wando Da Tattalin Arziki — Kwankwaso
  • Hadari Gabas… Tsugune Ba Ta Kare Ba A  Jam’iyyar PDP

Hallaka Kobo,

Kayan hadinsa: Sukari, Gyada. Ga kuma yadda ake hadawa:

A samu tukunya a dora a wuta, sai a zuba sukari a yi ta juyawa har sai sukarin ya narke sai a debo gyada dai-dai misali a zuba a yi ta juyawa har sai ya hade jikinsa. Sannan a samo tire a shafa masa man gyada. Bayan haka, sai a juye sukarin, idan ya dan sha iska sai a sa wuka a yayyanka yadda ake so, in an yi haka an kammala yin Hallaka Kwabo.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Hanjin Ligidi

Kayan hadinsa: Sukari, Tsamiya, ga kuma yadda ake hadawa:

A mataki na farko sai a samu jarida ko wata takarda mai girma a yayyanka a nade kamar yadda kaho yake, wato kasan ya yi tsini sama kuma ya bude, a sa kasa a roba ko wani abu mai fadi da zai dauki kasar a soka jaridar da aka nade din a cikin kasar. Sannan sai a jika tsamiya a ajiye a gefe, a samu tukunya a zuba sukarin a ciki a dora a kan wuta a yi ta juyawa har sai sukarin ya narke sai a dauko ruwan tsamiyar da aka jika a zuba a kai, za a ga ya taso sai a yi ta juyawa har sai ya hadu, sai a rika diba ana zubawa cikin jaridar da aka nada daidai gwargwado ana kuma saka masa tsinke a cikin kowanne.

Alewar Madara

Kayan hadi: Madarar gari, Sukari, da Filebo. Ga kuma yadda ake hadawa:

A mataki na farko sai a dora ruwa dan daidai a wuta sai a zuba sukari ya tafasa har sai ruwan ya yi kauri, sai a zuba filebo kadan a kawo madara ana zubawa ana tukawa kamar yadda ake tuka tuwo har sai ya yi tauri dai-dai misali, kar ya yi ruwa, sai a nemi tire a shafa man gyada sai a zuba dafaffen sukarin a kai a yanka daidai yadda ake so.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Jose Peseiro Yana Bin Nijeriya Albashin Wata Shida

Jose Peseiro Yana Bin Nijeriya Albashin Wata Shida

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.