Kwanan baya, wasu kamfanonin samar da kayan shayi masu tamburan kasar Sin sun jawo hankalin sassan kasa da kasa, sakamakon yadda suka fara sayar da hannayen jarinsu a kasuwar hannayen jari ta kasa da kasa. Baya ga haka, wasu kayayyaki masu tamburan kasar Sin na kara samun karbuwa a kasuwannin duniya. Har ma wasu kafofin yada labarai na kasa da kasa sun yi sharhin cewa, kayayyakin kasar Sin sun daina kwaikwayon wasu, suna bayyana halayensu na musamman a gaban jama’ar duniya.
Wadannan kayayyakin kasar Sin suna samun karbuwa a kasuwannin duniya ne sabo da fasahohin zamani da al’adu da ke tattare da su da ma yadda aka tsara fasalinsu, kuma hakan ya faru ne sakamakon cikakken tsarin samar da kayayyaki da yanayin kasuwa mai bude kofa da adalci a kasar, da ma yadda kasar ta dade tana dukufa a kan kirkire-kikire da kuma samun ci gaba mai inganci.
Shiga kasuwannin duniya da kayayyakin kasar Sin suka yi na bai wa masu sayayya na duniya damar samun karin zabi. A sa’i daya kuma, Sin na maraba da zuwan karin kamfanonin ketare masu ingantattun tamburan kasar, ta yadda za a yi koyi da juna da samun ci gaba tare, don al’ummun duniya su ci gajiyar dunkulewar tattalin arzikin duniya. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp