A kalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin kwale-kwale a hanyarsu ta zuwa wata kasuwa da ke Ugbo-Nla ta karamar hukumar Ilaje ta jihar Ondo.
LEADERSHIP ta samu cewa ’yan kasuwar sun yi hatsari ne a wani rafi, inda nan take suka rasa rayukansu, an ceto mutum daya da ransa sakamakon amfani da rigar ceto ta ruwa.
Bayan faruwar wannan mummunan lamarin, shugaban kungiyar masunta na kasa reshen jihar Ondo ta Nijeriya, Ambasada Orioye Benedict Gbayisemore, ya bukaci gwamnatin jihar da ta saka dokar ta bace kan tilasta amfani da rigar ceto ta ruwa acikin ruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp