Taron da dan takarar shugaban kasa na jami’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar da takwaransa na LP, Peter Obi ya sanya ana ta rade-raden cewa sun tattauna ne a kan yadda za su yi maja domin kwace mulki a hannun APC a 2027.
Atiku ya ce lallai wannan majar da za su yi abu ne mai yiwuwa a bisa dukkan alamu kuma suna da tabbacin cewa za a kai ga nasara don a cimma manufa.
- PAN Ta Karrama Matar Gwamnan Jihar Zamfara Kan Kula Da Mata Da Marayu
- Firaministan Sin Ya Sauka A Seoul Domin Halartar Taron Kasashen Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu
Idan za a iya tunawa bayan ganawarsa da Peter Obi, Atiku ya bayar da tabbacin cewa ba damuwarsa ba ne ya janye wa wani don a sami nasara.
Haka kuma Peter Obi ya gana da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.
Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar LP, Tanko Yunusa ya fitar da sanarwa bayan ganawar da ke cewa ziyarar na Peter Obi sun tattauna ne kan halin da kasa ke ciki.
Wani mai sharhin al’amuran yau da kullum, Julius Adegunna a bangarensa yana mai cewa wannan yunkuri abu ne mai kyau, wanda yake da shakku a cikinsa.
A cewarsa, mafi yawan ‘yan siyasan Nijeriya sun faye son ransu da kuma kwadayin mulki. Adegunna ya ce da zarar zabe ya gabato ne za a iya gane masu yi da gaske da masu neman abun duniya.
“‘Yan siyasar Nijeriya ba abun aminta ba ne. Sai dai kawai sadaukarwa ga wani fitaccen dan takara, idan ba haka ba kuma jam’iyyun adawa babu inda za su je.”
A nasa gudunmuwar, wani mai sharhi a kan al’amuran da suka shafi kasa, Bishop Hebert Eke¬chukwu ya dauki lamarin ne ya kai can baya abun da ke faruwa a tarihi na yin maja a tsakanin jam’iyyun siyasar Nijeriya tun lokacin samaun ‘yancin kai a 1960.
“Jam’iyyar siyasa takan bayyana manufofinta da kudurorinta da duk wasu abubuwa da zai kai ta ga samun nasarar a zabe.
“A tsakanin shekaru 1962 zuwa 1966, wasu jam’iyyu sun rabu sakamakon rikicin cikin gida da aka samu a jam’iyyar AG da NCNC da NPC suka zama jam’iyya guda daya mai suna UPP karkashin jagorancin Cif S.L. Akintola
“A shekarar 1983, jam’iyyun UPN da NPP da wasu sun hada kai suka yi maja don kwatar mulki a hannun NPN, amma shirin bai samu nasara ba.
“Maja da za a ce shi ne mafi nasara a shekarar 2013, a lokacin da jam’iyyun ANPP da ACN da CPC da wasu bangare na APGA a Jihar Imo suka zama jam’iyyar APC, wannan dai shi ne lokaci na farko da aka kayar da gwamnatin PDP.
“Amma a daidai lokacin da ake fuskantar zaben 2027, ina ganin adawa mara karfi. ‘Yan siyasar da ake da su a yanzu sun faye kwadayi da son rai da nuna kabilanci.
“Ina da shakku matuka ko za a iya samun nasara a wannan majar. Amma a batun maja ana bukatar hada karfi da karfe kamar yadda Cif Olesugun Obasanjo ya yi a wancan lokaci.”
Haka kuma a wancan lokaci ba wai kawai jam’iyyun adawa ba ne suka yi maja har da wasu gwamnoni da sanatoci da ‘yan majalisun wakilai na PDP suka fice a jam’iyyar suka shiga cikin majar.
Rarrabuwar kai ta yadda kowa yake ganin idan ya tsaya a karin kansa zai iya kai wa ga nasara, hakan ta sanya Atiku da Peter Obi da Kwankwaso kowa ya ja tunga a zaben 2023.