An yi wa Fira ministan Kuwait Sheikh Sabah Al-Khalid Al-Hamad Al-Sabah allurar riga-kafin cutar korona ta kamfanin Pfizer.
Fira ministan ya ce “A yau 24 ga watan Disamba mun fara yin allurar riga-kafin cutar korona. Don haka ina son godewa kwamitocin Ma’aikatar Lafiya da suka yi kokarin ganin yiwuwar hakan.”
Ya ce a jiya ne kasar ta karbi allurar riga-kafin Pfizer, kuma an fara bayar da ita a yau ga mutanen kasar.
Ya kara da cewa za a shafe tsawon watanni ana yin ta ta yadda dukkan al’ummar kasar za su samu damar yi.
Misali Daga Kebbi: Yadda Kananan Hukumomi Suka Shiga Uku A Nijeriya
Kamar dai yadda aka sani kananan hukumomi sune suka kasance...