Daga Khalid Idris Doya,
Biyo bayan sake bullar annobar Korona karo na biyu da sake karuwar adadin masu kamuwa da cutar a fadin kasar nan, wasu manyan jami’an gwamnati, da wasu fitattun mutane hadi da masu hannu da shuni a cikin kasar nan na fita kasashen waje domin yin allurar rigakafin Korona domin kariya daga kamu da cutar kamar yadda kafar yanar gizo ta ‘FirstNews Online’ ta nakalto.
Wadannan nau’in ‘yan Nijeriyan sun kasa jiran har sai lokacin da gwamnatin tarayya za ta bada damar kawo rigakafin Korona, domin a tunaninsu gwamnati ba ta shirya kawo rigakafin cikin Nijeriya nan kusa ba.
Har-ila-yau, an kuma gano cewa wasu manyan jami’an gwamnatin Nijeriya da na jihohi hadi da jiga-jigai su na kan shirye-shiryen yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje domin neman rigakafin Korona domin neman kariyan kai a gare su daga annobar.
Majiyarmu ta gano cewa, daga cikin irin wannan fitattun mutanen akwai Gwamnan Anambra Willie Obiano.
Obiano, an gano cewa, tunin ya kammala shirye-shiryen samun rigakafin nasa a kasar Amurka, na iya shiga cikin jirgi domin tafiya kasar Amurka nan da ‘yan makonni.
Kodayake tuni ma matar Gwamna Obiano, Madam Ebelechukwu, ta samu nata allurar rigakafin na Korona a Houston.
Wakazalika, gwamnoni da dama tare da iyalansu suna kan shirin fita kasashen waje domin samun rigakafin Korona a cibiyoyin lafiya daban-daban.
Wannan matakin dai na zuwa ne a ‘yan kwanakin baya da hukumar lafiya a matakin farko ta kasa (NPHDA) ta bada tabbacin cewa gwamnonin jihohi, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shi kansa shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari za a musu rigakafin Korona da za a nuna kai tsaye a gidajen talabijin domin karfafa wa ‘yan Nijeriya gwiwa su rungumi rigakafin Korona dari bisa dari domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Makonni kalilan da su ka wuce, tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar, ya bai wa ‘yan Nijeriya mamaki yayin da kwatsam aka tsinci hotunansa a kafafen sada zumunta yayin da ya isa Dubai ta Hadaddiyar Daular Larabawa inda aka gan shi ana masa allurar rigakafin Korona a wani cibiyar lafiya.
A yayin bullar annobar Korona karo na farko a shekarar da ta gabata, muhimmai kuma fitattun mutane ciki har da manyan jami’an gwamnati sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Korona.
Sannan kuma, wasu karin fitattun ‘yan Nijeriya ciki har da wasu gwamnoni masu ci, sun kamu da cutar amma cikin ikon Allah da taimakonsa ba su mutu ba sakamakon cutar inda suka samu warkewa bayan da suka amshi kulawar likitoci.
Daga cikin gwamnonin da suka tsira daga cutar sun hada da gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu; gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad; gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi; Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa tare da iyalansa.
Saura sun hada da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu; gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde; gwamnan jihar Benue da kuma gwamnan jihar Legas Olusola Sanwo-Olu.
Wasu kusoshin ‘yan Nijeriya da suka rasa rayukansu a sakamakon cutar tun lokacin da ta barke a karo na biyu sun hada da Babban Kwamandan rundunata ta shida, Manjo Janar John Olu Irefin; Abeokuta, fitaccen hamshakin dan kasuwan nan haifaffen Ogun, Dakta Bolu Akin-Olugbade da kuma tsohon gwamnan Legas a zamanin mulkin soja, Rear Admiral Ndubuisi Kanu.
A daidai lokacin da Korona ke kara ta’azzara wanda hakan ke haifar da karin rasar rayukan jama’a a fadin duniya ciki har da Nijeriya.
Wasu kasashe da daman gaske a fadin duniya tunin suka himmatu wajen ganin sun samu rigakafin Korona domin kariya ga rayukan ‘yan kasarsu.
Kamar yadda Babban Daraktan hukumar lafiya a matakin farko ta Nijeriya (NPHCDA), Faisal Shuaib, ya ce Nijeriya tana tsammanin dozun-dozun guda 100,000 na rigakafin Korona ta Pfizer da BioNtech zuwa karshen wannan watan.
Kasar wacce take tsammanin samun dozun na rigakafin Korona 42 a zango na fitu, domin tabbatar da jama’a sun samu rigakafin Korona yadda ya dace.
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da kwamitin karta kwana kan tabbatar da tsaron zuwan rigakafin Korona mai mambobi 18 da za su tabbatar da rigakafin ya zo cikin kwanciyar hankali.
Sai dai kuma wasu manyan jami’an gwamnati da iyalansu tare da wasu jiga-jigan ‘yan Nijeriya sun ki zaman jiran har sai gwamnati ta kawo rigakafin, inda suka hanzarta fita kasashen waje domin neman rigakafin, yayin da wasu ma suke shirin fita domin neman rigakafin a kasashen waje.
Sai dai kuma wasu ‘yan Nijeriya na sukan irin wadannan nau’in ‘yan Nijeriyan da suke fita abunsu domin neman rigakafin a kasashen waje, suna masu cewa son kan shugabanin ya yi yawa sosai.