Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bai wa hukumar tsaro ta farin kaya DSS damar tsare Tukur Mamu – Mai shiga sasanci tsakanin iyalai da ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Kaduna, har tsawon kwanaki 60.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN, Alkalin kotun, Nkeonye Maha, ya bada damar tsare Mamu ne a ranar Talata a wani kudurin da lauyan hukumar DSS, Ahmed Magaji ya gabatar.
A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1617/2022 a ranar 12 ga watan Satumba, hukumar DSS ta bukaci kotun da ta amince da bukatar tsawaita tsare Mamu domin ta samu damar kammala bincike.
Mamu, mai taimaka wa fitaccen Malamin musulunci, Ahmad Gumi, ya shiga tattaunawa tsakanin Iyalai da ‘yan bindiga ne don ganin an sako mutanen da aka sace a wani hari da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, a watan Maris din 2022.
Da yake tsokaci game da kama shi, Gumi ya ce tsare Mamu aikin ta’addanci ne, don haka hukumar DSS ta gurfanar da shi a kotu ko kuma ta sake shi.
Da yake mayar da martani a wata sanarwa a ranar Lahadi, Peter Afunaya, mai magana da yawun hukumar DSS, ya ce hukumar DSS ba za ta damu da wasu kalaman batannci ba kan aikinta.