Wata kotu a garin Jos na Jihar Filato ta daure wani dan kasuwa mai suna Bashiru Aliya mai shekaru 28 a gidan yari har na tsawon watanni tara bisa samunsa da laifin satar kwali biyu na kayan yaji na kudi Naira 98,500.
Alkalin kotun, Shawomi Bokkos, ya yanke wa Aliyu hukuncin ne bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kamar yadda Kamfanin Dillancin labarun Nijeriya ya ruwaito.
- ‘Yansanda Sun Gargadi NNPP Da APC Kan Shiga Zanga-zanga A Kano
- Gwamnatin Kano Ta Dawo Da Ma’aikatan Da Ta Dakatar Da Ganduje Ya Ɗauka Aiki
Sai dai Bokkos ya ba shi zabin biyan tarar Naira 20,000 tare da umartar sa da ya biya wata Naira 120,000 a matsayin diyya ga wanda ya kai karar.
Tun da farko, dansanda mai gabatar da kara, Sufeto Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa an kai karar ce a ranar 4 ga watan Agusta a ofishin ‘yansanda na Railway da wanda ya shigar da kara, Moses Agbo.
A cewar NAN, mai gabatar da karar ya ce wanda ake tuhumar ya hada baki da abokinsa, ya kuma ya saci kayan a shagon wanda ya shigar da kara da ke kasuwa.
Gokwat ya ce laifin ya saba wa tanadin kundin hukunta manyan laifuka na Filato.