Wata Kotun Majistare mai lamba 70 a jihar Kano ta tsare wasu mutane hudu a gidan yari bisa samun su da laifin hada baki wajen aikata sata.
Wadanda ake zargin, Nuhu Auwalu, Yakubu Bala, Emmanuel Luka, da Safianu Abdullahi, sun yi awon gaba da birki na jirgin sama guda 80 daga kamfanin jiragen sama na Azman a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA) da ke Kano.
- Hamas Ta Amince Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Isra’ila
- Ranar Tunawa Da Mazan Jiya: Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Inganta Rayuwar Iyalan Jaruman Da Suka Rasu
A cewar takardar tuhumar, jami’in tsaron kamfanin jiragen sama na Azman ne ya hada baki da wadanda ake tuhuma domin aikata satar, wanda wani ma’aikacin kamfanin Otaru Bashir ya tona musu asiri a ranar 11 ga watan Disamba, 2024. Sai dai wadanda ake zargin sun musanta zargin da ake masu.
A zaman kotun, an bayyana cewa an samu birki guda uku a hannun Yakubu Bala a yayin binciken.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Faruk Ibrahim Umar, ta tasa keyar wadanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali, sannan ta sanya ranar 11 ga watan Fabrairun 2025 mai zuwa domin ci gaba da sauraron karar.