Babbar Kotun Majistare da ke zama a Ado-Ekiti shalkwatar Jihar Ekiti, ta hana Chibike Nwakedi mai shekara 43, cewa kada ya yi wa matarsa Blessing magana har tsawo makonni biyu har sai lokacin da suka dawo kotu domin ci gaba da sauraren kararsu.
Babban Alkalin majistare Dolamu Babalogbon ya ce ma wanda aka yi karar kada ya yi magana da matarsa, ko ya kira ta ta waya ko ya je kusa da ita idan ba da izinin lauyanta ba.
- Ci Gaban Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
- Kasar Sin Na Kira Ga Amurka Ta Daina Danne Kamfanonin Waje Ba Bisa Adalci Ba
Dansanda mai gabatar da mai laifin Sufeta Sodik Adeniyi, lokacin da yake gurfanar da shi, ya shaida wa kotu cewa ranar 3 ga Maris da misalin karfe takwas a Ado-Ekiti, Nwakedi ya ci mutuncin matarsa lokacin da ya buge ta da katako wanda hakan ya yi sanadiyar karyewarta.
Sufeta Adeniyi ya ce halin da mutumin ya nuna na iya kawo rashin zaman lafiya, sannan ya kara shaida wa kotu cewa abin da mutumin ya aikata ba karamin laifi bane idan aka yi la’akari da sashe na 186, da 181 (D) na dokar Jihar Ekiti ta shekarar 2021.
Sai dai Lauyan da yake kare mai laifin Barista Gbenga Ariyibi ya yi kira da kotun ta ba da belin wanda yake karewa, inda ya kara da cewa ba zai gudu ba, kuma zai kawo sahihin wanda zai tsaya masa.
Babban Mai shari’a Dolamu Babalogbon ya ba da belin wanda ya aikata laifin a kan kudi Naira 50,000 da mutum biyu da za su tsaya masa, suma da Naira 50,000, ya kuma tsaida ranar 28 ga Maris 2024 domin ci gaba da sauraren