A sanarwar da rundunar ta fitar ta ce bayan an gudanar da bincike kuma an samu dan sandan da ke gadin gidan tsohon shugaban kasan da hannu cikin satar da aka yi a gidan.
Rundunar ta kara da cewa, an gurfanar da wanda ake zargi da aikata laifin, Sajan Musa Musa, a gaban kuliya a kotun Majistare da ke unguwar Wuse ne yau a Abuja.