A makon nan ne dai babbar kotun tarayya da ke Kano ta ce tana da hurumin sauraren karar da aka shigar gabanta na take hakkin dan Adam da tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da Aminu Babba Dan’agundi suka shigar. Wannan hukuncin ya biyo bayan mayar da Sarki Muhammad Sanusi II kan kujerarsa.
Kotu ta bayar da wani umarnin da ta hana Gwamna Abba Yusuf na Kano mayar da Sanusi kan mukaminsa har sai an warware wata karar da aka shigar a kan batun dawo da Sarki Sanusi. Haka kuma umurnin ya nuna adawa da soke masarautun Bichi, da Gaya, da Karaye, da kuma Rano—a karkashin wani kudiri da majalisar dokokin jihar ta zartar a baya.
- Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yin Katsa-landan A Harkokin Kano
- Tsautsayin Sallah: An Tsinci Gawar Wata Mata A Gidan Malamin Tsibbu A Kano
Masanin shari’a Femi Falana ya bayar da hujjar cewa bisa ga sashe na 254 (C) (1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, kotun masana’antu ta kasa ba ta da hurumin shari’ar sarauta.
Ya jaddada cewa, duk da cewa sarkin da aka tsige ba tare da an yi masa adalci ba yana da hakkin a yi masa shari’a, babban abin da ake da’awa a wannan shari’ar bai kamata ya dogara ne kan aiwatar da muhimman hakkokinsu ba, sai dai a kan wani batu na musamman na masarautu, wanda ya sabawa hurumin babban kotun tarayya.
Shigar da babbar kotun tarayya kan takaddamar tsige Sarki Aminu Ado Bayero da mayar da Sarki Sanusi Lamido Sanusi kan mukaminsa na kamanceceniya da wani mataki da ya ci karo da hukuncin da kotun koli ta yanke kan shari’ar Sarki Tukur da gwamnatin jihar Gongola a shekarar 1987 4 NWLR (117) 517.