Daya daga cikin limaman rukunin gidaje ‘yan majalisa na Apo, Imam Ibrahim Lawal Usamah, ya bayyana cewa kowanne dan siyasa akwai abin da ya sa shi shigar ta.
Imam Usamah ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai kan al’amarin siyasar na wannan zamani, wanda ya sha bamban da irin salon siyasar shekaraun da suka gabata.
Ya ce yawan ‘yan takarar shugaban kasa a yankin arewa babu wata matsala na rarraba kuri’un daga yankin, idan mutum ya kalli tsarin siyasar Nijeriya ai duk wannan ba wata matsala bace, cikin minti ashirin ko awa daya zuwa biyu ana iya maganin ita matsalar, saboda kowanne dan takara akwai abin da ya kawo shi cikin siyasa.
Ya kara jaddada cewa akwai wanda ya zo ne neman kudi, sai kuma wanda shi al’ummarsa ce manufarsa, amma mafi yawancin ‘yan siyarsa a halin yanzu kudi suke nema da kuma mukammai, tana iya yiyuwa da an kira su don yin sulhu musamman ma ‘yan Kudanci aka nuna masu batun addini da mukaman da za su samu, duk za su iya janyewa tare da marawa wanda suke ganin zai iya kaiwa ga ci, su kuma za su samu damar cimma manufarsu.
Bugu da kari, ya yi karin bayani ya ce wannan a bangaren kudu kenan, yayin bangaren arewa akawi wadanda za su iya janyewa domin wani dalili, ko za su ki janyewar saboda rikicinsu da wasu gwamnoni.
A namu tunanin idan suka ga ba za su kai labarai ba, ko kuma suka ga cewa idan suka bata kuri’ar arewa aka samu matsala, maimakon abin ya zama masu farin jini, sai ya zama bakin jini a gare su.