Majalisar wakilai ta yi karatu na farko a kan kudirin dokar da ta gabatar na gyaran kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, domin gabatar da wa’adin mulki daya na shekara 6 ga shugaban kasa da gwamnonin jihohi da shugabannin kananan hukumomi.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ideato ta arewa /Ideato ta Kudu a Jihar Imo, tare da wasu ‘yan majalisa 50 ne suka gabatar da kudirin da na nufin rage kudaden da ake kashewa kan zabe ta hanyar rage wa’adin wadannan ofisoshi.
- Tsaro: Gwamnatin Tinubu Ta Kashe Naira Tiriliyan 3.2 A Shekara Daya
- Martani: Ba Hannu Na A Kisan Sarkin Gobir, Sharri Ne Na Ƴan Adawa – Hon Boza
Sauye-sauyen na da niyya shafar sashe na 7, 135, 137, 180, da 182 (1) na kundin tsarin mulki na 1999.
Sashi na biyu na kudirin ya nemi a gyara sashe na 7 na dokar ta hanyar shigar da wani sabon sashe na 5 bayan karamin sashe na 4, wanda sashe na 5 ke cewa, “Duk wani mai rike da mukamin shugaban karamar hukuma zai bar ofishinsa a lokacin da wa’adinsa ya kare na shekaru 6 daga ranar da aka zabe shi.”
Sashe na 3 na kudirin yana neman a gyara sashe na 135 (2), (2A) da (3) na kundin tsarin mulki domin maye gurbin kalmar “hudu” zuwa “shida”.
Dangane da tanadin karamin sashe (1) na wannan kudirin, shugaban kasa zai bar ofishinsa a karshen wa’adin zangon shekaru shida (6) lokacin da aka zabe shi. Idan kuma aka zabe mutum a matsayin shugaban kasa har aka rantsar da shi a karkashin wannan tsarin, to za a kara gudanar da zabe, sannan za a yi la’akari da lokacin da aka fara rantsar da na farko ne.
Haka kuma kudirin ya bayyana cewa idan ana fama da yaki a Nijeriya, shugaban kasa yi la’akari da haka ya ki gudanar da zabe, amma majalisa na iya kari sama da shekara 6 lokaci bayan lokaci bisa karamin sashi na 2, sai dai karin ba zai wuce wata shida ba a ko wani lokaci.
Sashe na 4 na dudirin yana neman gyara sashe na 137 na kundin tsarin Nijeriya ta hanyar share sakin layi (b) da sake lambobi.
Sashe na 5 na kudirin da aka gabatar na neman gyara sashe na 180 na tsarin mulki ta hanyar goge wasu kananan sashe na 2 da na 3 tare da maye gurbinsu da sabon sashe na 2 da 3.