Kungiyar Kididdiga Da Tantance Farashi Ta Ziyarci Wasu Makarantun Jihar Kano

Kwanakin baya ne kungiyar kididdiga da tantance farashin kayayyaki irinsu fili da gidaje da kamfanoni. “Estate Surbeyors and Baluers” ta jihar Kano karkahin shugabancin Mista Salam Oyewumi, ta gudanar da taron ta na shekara shekara inda ya samu halarta da dama daga cikin ‘yan kungiyar maza da mata .

Da yake gabatar da jawabinsa ga manema labarai bayan kamma taron Mista Salam Oyewumi ya nuna matukar farin ciki da yankungiyar suka amu damar halartar taron. Ya ce makasudin shirya taron shi ne domin a hadu atattauna cigaba da kuma matsalolin da suke fuskanta ajihar Kano,inda ya kara da cewa  zai yi bakin kokarinshi domin ganin harkar Estate a Kano ya samu gidin zama tare da sanar da al’ummar jihar muhimancin wannan fanni tun daga makarantun sakandare da suran muhimman wurare zaman al’umma  wannan ya sa  daga lokacin daya hau karagar shugabancin kungiyar suka fara kai ziyara wasu daga cikin makarantun sakandaren jihar kamar Kwalejin Yandutse, da kuma wata makarantar  sakandare dake garin Bichi, da sauran makarantun jihar wannan ziyara na fadakar da daliban zai cigaba kafin ya kammala shugabncin kungiyar na shekaru biyu da izinin Allah.

Bayan kai ziyaran ga wasu makarantun jihar sun kai irin wannan ziyara ga kwamashinonin filaye da safiyo, da na yada labarai da kuma wasu daga cikin manyan jam’ian gwamnatin jihar akan muhimmancin kungiyar.

Suna fatan gwamnatin jihar za ta shigo da su domin bayar da shawarwari musamman akan filaye da gidaje mallakin gwamnatin. Gwamnatoci idan suna bukatar gine gine irin na zamani sukan tuntubesu domin bayar da shawarwari, da kuma duk wanda yake son gina gidaje domin ba da haya a cewarshi sune suka san kimar gidaje da filaye tare da kamfanoni, sannan kuma duk wanan abu da suke gudanarwa suna yin shi ne a bisa dokokin kasar nan .

Sai dai ya koka game da yadda mutanan Arewain kasar nan ba su fahimci wannan fanni sosai ba idan ka kwatanta da na kudancin kasar nan da suka yi wa na Arewaci fintinkau, amma duk da haka a kwai kwararru a wannan fanni a jihar Kano fiye da shekaru  30 yayin kuma da har ila yau akwai yankungiayar kimanin 90 a jihar Kano .

Kuma duk wanda ya kware awannan fannin zai iya kiyasce kudin gida masana’antu da filaye da sauran kaddarori. Daga karshe ya ya shawarci yan kungiyar da su kara ba shi dadin kai domin kaiwa ga samun nasara  sannan kuma kofarshi abude take wajen karbar shawarwari matukar suna da anfani  ga cigaban kumgiyar da al’umar jihar Kano baki daya.

 

Exit mobile version