Kungiyar Musulunci Ta JNI Ta Taya Daukacin Musulmi Barka Da Sallah

JNI

Daga Ahmed Muh’d Danasabe, Lokoja

Babban kungiyar Musulunci ta Jama’atu Nasril Islam( JNI) mai hedikwata a Kaduna tana yiwa daukacin al’ummar musulmin Nijeriya murnan babban Sallah.
Sakataren kungiyar ta JNI, Dakta Khalid Aliyu ne ya sanar da hakan a Kaduna.
Kamar yadda sanarwan tace, Kungiyar ta JNI karkashin shugabamcin Mai Alfarma, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na taya daukacin al’ummar musulmi murnan babban Sallah.
Sanarwan tayi bayani kamar haka” Muna rokon Allah Ya sanya sunayenmu cikin wadanda  zai  karbi ibadunsu da layyarsu cikin wadannan kwanaki.
“Allah baya bukatar jinanen abinda muka yanka ko namansu” kamar yadda Aliyu yace.
Sakataren kungiyar ta JNI ya kuma tunatar da al’ummar musulmi da suyi Azumi a yau Litinin na yinin ranar Arafat.
” Kada mun manta da ambaton Allah a koda yaushe, mu gode masa bisa ni’imarsa” Cewar Aliyu.
Ya kuma yi kira ga sauran yan uwa musulmi da suyi taka tsan tsan da hali na tsaro,gami da bin dokar karkarewar numfashi ta cobid 19( Korona).
Yace za a iya amfani da jami’an tsaro  wajen tabbatar da kawo zaman lafiya a wannan kasa.
” Muna kira ga Gwamnati data kara himma wajen daukar matakai na tsaro” Inji Dakta Aliyu.

Exit mobile version