Gamayyar Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban Jami’ar Bayero waɗanda suka kammala karatu a shekarar 2015 a Sashen Koyar da Harsuanan Nijeriya da Sashen Kimiyyar Harshe da Harsunan Ƙasashen Waje na Jami’ar, sun karrama abokin karatunsu da ya zama zakara wajen zama mutum na farko a ajin su da ya kammala digiri na uku a ɓangaren Kimiyyar Harshe, Dr. Sani Dauda Ibrahim.
Taron an gabatar da shi ranar Asabar 10, ga Mayu 2025 a dakin cin abinci da shaƙatawa na Albaik Chicken da ke titin zuwa Gwarzo a jihar Kano. A yayin taron walimar, tsofaffin ɗaliban sun karrama Dr. Sani Dauda Ibrahim a matsayin gwarzo kuma wanda ya yi fice ajin 2015 da wata shaidar girmamawa ta musanman kan nuna ƙwazo wajen zama mutum na farko da tarihin ɗaliban ba zai manta da shi ba.
- Tsofaffin Ɗaliban BUK Sun Yaba Wa Masarautar Hausawan Turai Kan Naɗa Ma’ajin Hausawan Turai
- Ɗaliban Jami’ar Bayero ‘Yan Ajin 2015 Sun Zamanantar Da Ɗakin Karatu Na M.A.Z Sani
A jawabin shugaban taron kuma Sakataren Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban, Muhammad Bashir Amin, ya godewa Allah bisa cikar burinsu na samun damar shirya walimar karrama abokin na su da ya yi fice a tsakaninsu tun lokacin da suke karatu tare da shi a matakin digirin farko a Jami’a, ya kuma yi fatan ci gaba da shirya makamancin irin wannan taruwa girmamawa ga mambobin ƙungiyar a fannonin rayuwa da dama, da fatan nasarar Dr. Sani Dauda Ibrahim ya samu ta amfani ilahirin ɗalibai da jami’ar da dukkan al’umma baki ɗaya, a jawabin nasa ya godewa shugaban Ƙungiyar Alhaji Hassan Baita Ubawaru (Ma’ajin Hausawan Turai) da ‘yan kwamitin shirya taron da sauran mambobin ƙungiyar kan irin haɗin kai da gudunmawar da suke bayarwa a koyaushe wajen ci gaban ƙungiyar.

A nasa jawabin, Dr. Sani Dauda Ibrahim, ya nuna farin cikinsa tare da godewa shugabancin ƙungiyar bisa karrama shi da suka yi wajen shirya liyafar ta ya shi murna da suka yi, ya ce nasarar ba ta shi ce kaɗai ba, ta kowa da kowa, saboda tabbas bai san wahalar karatu ba saboda Allah ya shiga cikin lamarinsa sosai tare kuma da addu’a iyaye da dafawar malamansa da abokan karatunsa, ya kuma bayyana cewa a nasa ɓangaren ya ci alwashin ci gaba da bayar da tasa gudunmawar wajen ci gaban ƙungiya tare da tabbatar da dorewar zumunci a tsakanin mambobin ƙungiyar.

Shugaban Sashen Kimiyyar Harshe na Jami’ar Bayero, Dr. Tijjani Shehu Almajir, wanda shi ne ya jagoranci duba aikin Dr. Sani Dauda Ibrahim, ya bayyana ƙwazo da hazaƙar da ɗalibin ya ke da ita a matsayin wani abu da suke alfahari da shi.
“Haƙiƙa muna alfahari da Dr. Sani Dauda Ibrahim da wannan ajin naku, musanman cewa akan ku na fara koyarwa a jami’a, kuma haɗin kan ‘yan wannan ajin ya zama na daban a cikin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, musanman saboda ayyuka da kuka gabatar na ci gaban ilimi a jami’ar Bayero da yadda kuke damuwar da al’amuran ilimi” cewar Dr. Almajir.
Taron ya samu halartar Dr. Maimuna Isma’il da ke koyarwa a sashen da sauran mambobin ƙungiya da ‘yan uwa da abokan arzikin Dr. Sani Dauda Ibrahim da aka karrama a wajen taron.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp