An Bayyana kungiyoyin Matasa a karamar hukumar Mani ta jihar Katsina sun taka rawar gani fiye da dan majalisa mai wakilitar karamar hukumar a zauran majalisar dokoki ta jihar Katsina, Honarabule Aliyu Sabi’u Muduru.
Hon. Abubakar Kabir Jani, shi ne mai wakili a zauren majalisar matasa ta kasa, mai wakiltar karamar hukumar Mani, ya bayyana cewa kokarin da ya ke na kawo wa karamar hukumar Mani da matasanta cigaba mai dorewa, ya zarce na dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Mani a zauren majalisar dokoki ta jihar Katsina, Alhaji Aliyu Sabi’u Muduru.
Hon. Abubkar Jani ya yi zargin cewa idan aka duba irin rawar da kungiyoyin matasa suka taka wajan fadakar da al’umma wasu muhimman ayyuka lallai babu shakka sun zama makwafin wakilin karamar hukumar a zauran majalisar dokoki.
A cewarsa taron tattaunawa na karawa juna sani da ake yi da matasa daga lokacin zuwa lokaci ya bada matukar ma’ana da tasirin idan aka yi duba ta bangaren ganin matasa sun zamo masu dogaro da kansu da kuma ganin sun samu ilimi domin fita daga kangin jahilci da bangar siyasa wanda ta zama ruwa dare gama duniya a wannna lokaci..
“Ina kira ga al’umma wannnan karamar hukuma ta mu, su cigaba da ba wadannan kungiyoyin matasan hadin kai da duk ya dace, saboda kokarin da suka yi a zahiri, ya kusan fi wanda dan majalisa mai wakiltar su ya gudanar duk da suna fuskantar kalubale na kudi. Kuma Ina kira ga Alhaji Aliyu Sabi’u Muduru, wanda har kakakin majalisar ya yi, da ya maido hankalin shi, wajen ganin ya kawo wa karamar hukumar da ya ke wakilta cigaba mai dorewa da kuma samawa matasa ayyukan yi.” Inji shi