Kungiyoyin Agaji Sun Daura Damarar Ceto Al’ummar Nijeriya Daga Kunci – Dakta Saddiku

Hukumar UNICEF ta bayyana cewa, Mutanan Najeriya su suka fi kowa zama a cikin kuncin rayuwa a duk fadin Afirka.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wani bincike da ta fitar. Ta ce kasar Najeriya su suka fi kowa yawan Jama’a a Afrika, amma abin haushi suna rayuwa ne ba tare da sun sami damar da ya kamata su samu a rayuwa ba.
Ga cututtuka wanda wasu kasashen Afrikan sun riga sun kawar da ita, amma su har yanzu ba su iya kawar da cutar ba. Misali kamar cutar Poliyo, ga shi yawan Jama’ar kasar kara nunninkawa ya ke yi. Binciken ya ce, wannan ba karamin kalubale ba ne ga hukumomin Najeriya.
Hukumar ta bayyana cewa, tana nan tana iya kokarinta wajen ganin an shawo kan wannan matsalar a Najeriya. Ta ce za mu hada kai da sauran kungiyoyi masu taimakon Al’umma don mu ga yanda za a magance wannan matsalar da ta tunkaro.
Cikin kungiyoyin akwai sama da mutum dubu dari biyu da suka dauki damarar magance matsalolin da ke addabar al’umman Nijeriya.
Hukumar UNICEF ta ce wadanan kungiyoyin sun kuduri aniyar shiga lunguna na karkara da biranai domin fazakar da al’umma yanda za su rika taimakawa kawunansu.
Sannan za su kara fadakar da al’umma game da mahimmanci alluran rigakafin cutar shan’inna da yake addabar kananan yara da ke rayuwa a karkara.
UNICEF ta kuduri aniyar taimakawa mata da yara da ke rayuwa a karamar hukumar Gwoza, wadanda matsalolin rayuwar yau da kullum da ma matsalar ruwan sha ya addaba.
Ta kara da cewa, dubban mutanen da suka sadaukar domin taimakawan za su fadakar da Shugabannin kabilu da na Addinai wajen fahimtar da su mahimmancin rigakafin.
Shi ma da yake Magana, Dakta Anis Saddiku ya ce; akwai sama da kauyuka kimanin 350 da suke bukatar samun alluran rigakafin cutar poliyo.
Ya kara da cewa, hukumar UNICEF ta tantance mutanen da za su shiga wannan aikin na ceto al’umman Nijeriya daga cikin kuncin rayuwa.

Exit mobile version