Sakamakon yawaitar juyin mulkin sojoji a Nahiyar Afirka a ‘yan tsakanin nan, LEADERSHIP Hausa ta tattauna da Shugaban Cibiyar Bincike da Nazarin Harkokin Dimokuradiyya (CEDDERT) da ke Zariya, FARFESA MUHAMMAD MUSTAPHA GWADABE, dangane da abubuwan da ke ingiza hakan. Ya fede biri har bindi tare da wakilinmu, IDRIS UMAR ZARIYA, kamar haka:
Ko Farfesa zai gabatar wa da masu karatu kansa?
Sunana Farfesa Muhammad Mustafa Godabe, Shugaban Cibiyar Inganta Demokuradiyya da bayar da horo a kan yadda za a fahimce ta, a kuma gudanar da ita.
Yaya wannan cibiyar ke kallon danbarwar juyin mulkin da sojoji ke yi a wasu kasashe na Afirka a halin yanzu?
Abubuwan da suke faruwa a Afirka, musamman a yammacinta ko a Sahel da muke magana, abubuwa ne wadanda mun jima muna aiki a kansu, sannan kuma mun dade muna jan kunne a kansu, ba don wani abu ba, sai don nuna wa mutane cewa; ita fa demokuradiyyar nan akwai a binda yasa ake yin ta.
Ko shakka babu, ana yin demokuradiyya ne domin samar da wani abu, ta hanyar bayar da dama ga dukkannin dan kasa ya sanya hannu wajen yadda ake tafiyar da mulki, tun daga kan zaben shugaba har zuwa yadda ake aiwatar da mulkin. Ma’ana, demokuradiyya wani yanayi ne na mulki wanda ake da bukatar kowa ya tofa albarkacin bakinsa.
Haka tsarin yake, amma yadda ake so a yi shi ne, tunda ba za ku iya tara mutane baki-daya a wuri guda ba, za ku iya zabar wadanda za su iya wakiltar ku, wadanda idan suka je wajen kamar ku ne a wurin. Haka ka’idar abin ya kamata ya zama,ka ga a nan ya nuna cewa, ba maganar a yi amfani da wani abu da niyyar a dauki hankalinka ka je wajen ba, shi yasa aka fi so a kai mutane masu amana da gaskiya, wadanda za su kula da dukkanin abin da ya shafi rayuwar wadanda suke wakilta kamar yadda doka ta zaiyana.
Wadannan su ne abubuwan da aka rasa, shi yasa tsawon lokaci muke fadawa mutane gaskiyar wannan al’amari. Sa’ar da aka yi a nan Nijeriya shi ne, na daukar tsawon lokaci ana so a yi wannan demokuradiyya, tun bayan samun ‘yancin kai. Sai dai ba a samu yadda ake so ba, musamman jamhuriya ta farko, al’amarin lalacewa ya yi har sai a jamhuriya ta biyu, bayan Shugaban Kasa na lokacin; Marigayi Shehu Usman Aliyu Shagari, ya kammala wa’adinsa na farko, aka sake yin zabe a karo na biyu, ba a je ko’ina ba sojoji suka yi juyin mulki.
Daga nan, an dauki tsawon lokaci sojoji na yin mulki, wanda hakan shi ma ya kawo tarnaki iri daban-daban. Daga wannan lokacin ne kuma, aka samu yanayin dorewar demokuradiyya baki-daya.
Har ila yau, tsarin wannan demokuradiyya ya dauki lokaci mai tsawo, wato ta yi tasiri har zuwa lokacin da aka samu canjin yanayi, gwamnati na kan mulki aka zo aka kwace mulkin daga hannunta. Wannan shi ne yake nuna alamar an fara dorewa kenan, amma babban kuskuren da ‘yan siyasa ke yi, wanda mu kan fada musu lokaci zuwa lokaci shi ne, a tsaya a dubi siyarar nan, domin kuwa wadanda ke kan mulki sun fi kowa jin dadinsa, don haka me ya sa ba za su tsaya su yi abin da ya dace ba, domin yanayin mulkin nasu ya ci gaba?
Bugu da kari, babban kurakuren da ake samu daga wurin ‘yan siyasa su ne, mafi yawan alkawuran da suke yi ba sa cikawa. To, idan ka duba wannan kusan a dukkanin Kasashen Afirka da ake aiwatar da demokuradiyya abin da ke faruwa kenan, illa kawai kasashen da demokuradiyyar ta balaga, kamar Kasar Amurka da Ingila.
Wadannan dalilai ne suka sanya a wadannan kasashe namu, sakamakon koma bayan da muke dashi a bangare, yasa dole sojoji shigowa cikin al’amarin su yi juyin mulki, domin wasu dalilai da suke gani na mayar da kasa baya ko wasu wahalhalu da da ake fuskanta a kasar, inda za ta kai ga rasa rayukan wasu sojojin sakamakon yaki da ‘yan ta’adda da sauran makamantansu. Ko shakka babu, wannan na sanya sojoji samun damuwa a cikin kasa, kana matsayin soja amma ba ka da kwanciyar hankali, kullum sai aikin tsaro, me nake nufi da aikin tsaro?
 An yi tashin hankali can; an yi a nan, yanayin gwamnati bai ba da zaman lafiya ba, yadda shi kansa soja zai zauna ya kara kwarewa a harkar da ta shafi sake kwarewa a fannin tsaro, a’a, sai dai kullum yana kai kansa ga halaka, yanayin demokuradiyya ya haifar da damuwa, to wannan shi ne yake faruwa a dukkanin kasashenmu na Afirka, kuma wannan shi yake sa sojoji su taso su yi abin da suka ga ya kamata su yi.
Ganin cewa cibiyarku tana nazari a kan al’amuran da suka shafi tsaro, lafiya da sauran makamantansu, ko akwai wani nazari da ta yi domin samun mafita?
Wato ka san ba ka tunanin mafita har sai ka san abin da ya faru. Ka ga kamar shekaru goma sha da suka wuce, mun yi wani dogon bincike da ya kai mu ga bangarori da dama, wanda a kan samu damuwa. Misali, mun je Birnin Gwari da Dansadau cikin Jihar Zamfara, sannan mun kuma je Katsina tun ma a lokacin da ake zaton rigima ce tsakanin Fulani da Manoma.
 Aikinmu na farko shi ne, tara dukkanin shugabanni a kasar nan tare da shaida musu cewa, mun yi bincike mun gano cewa ba maganar rikici ba ne tsakanin Manoma da Makiyaya, wani abu ne wanda sai an tashi tsaye, sannan kuma wannan abun shi ne ya haifar da abin da ake ciki a halin yanzu, a lokacin wato mutane ne suka tashi da wani tunani na satar shanu, sai ya zama ya talauta Fulani sun shiga cikin babbar fitina da tashi hankali.
A daidai wannan lokacin, mutane ne ba su gane ba yawancin Fulanin nan da ake tafiyar musu da shanu wasu ba mallakarsu ba ne; suna karbowa kiwo ne, don haka mutum ya karbo kiwo ya taho nesa saboda harkar ciyawa da suke yi ba harka ce ta sayo wa shanu abinci ba da kudi ba, harka ce ta a bi daji a ciyar da su da abin da Allah ya hore.
Duk lokacin aka ce, kana Bafulatani ka karbo kiwon dabbobin mutane, sai aka zo aka kwace; ka ga babu yadda za a yi ka iya komawa gida, sannan kuma ba ka saba rayuwar birni ba, saboda haka a dajin nan za ka zauna, kuma me yake faruwa a dajin? A nan ne za ka hadu da mutane daban-daban, musamman mugaye wadanda idan zaman gari ya gagare, sai su koma daji.
Haka zalika, a cikin dazuzzukan nan namu; akwai bangarori daban-daban da wannan kasa ta kebe, sai ya kasance gwamnati ta yi sakaci, ga shi ta kebe wajen, ko a inda ‘yan Boko Haram suke a Maiduguri ai irin kebabben wurin ne.
A wurin duk wani abu na rayuwa akwai shi, akwai ruwa mai kyau tare da halittu nau’i iri daban-daban, sai ya kasance cewa, wadannan mutane babu inda suke taruwa sai irin wadannan wurare, an saci shanu an wuce da su kudu an sayar da su, an samu dukiya, an zo dukiyar nan da aka samu ba cikin birni za a je a zuba ba, ba gidaje za a je a gina ba, ba motoci za a saya ba, shi yasa muka ce ba magana ce tsakanin Makiyaya da Manoma ba. Illa kawai magana ce ta akwai mutanen da suka dauki wannan al’amari a matsayin sana’a.
Ka je ka yi fashi ka kwato shanu ka samu kudi, ka zo ka yi bushasha ba ka samu kudi ka zo ka yi wani abun kirki ba. Daga nan wannan al’amari ya fara, wannan abin ne ya sa Fulani suka shiga cikin wani mummunan hali na ha’ula’i a rayuwa, sai kuma ya zo da kamar wani abu wanda aka shirya, sai ya kasance ana hada shi da shaye-shaye.
Duk wanda ya kasance cewa akwai dukiyar mutane a hannunsa, an bi shi an kwace ko kuma ga dukiya a hannunsa ya rasa ta baki-daya, babu abin da ba zai iya aikatawa ba. Akwai wani a cikinsu da muka yi wa tambayoyi ya ba mu labarin cewa, a gabansa an zo a kwashe masa shanu, an yi zina da ‘ya’yansa da iyalansa a gabansa, mutumin nan hauka ne kawai bai yi ba, an sa mutane a cikin mummunan hali na damuwa, sannan an zo an sa mutane a cikin shaye-shaye, wannan shi ne sanadiyar shigar mu halin da muka samu kanmu a ciki.
 Shi ya sa wasu mutane suka samu makamai, wadanda ba ma maganar su je su yi kiwo ba, ko wani abu makamancin haka, tun da dai da farko gwamnati ba ta kula da su ba, ba su da wutar lantarki, ba su da ruwa, ba su da titi, ga shi suna biyan jangali suna ba da dukkannin abubuwan da gwamnati ta bukata daga gare su. Don haka, wannan shi ne dalilin da ya sa aka samu fitinannu a cikinsu aka hure musu kunne, suka samu makamai na ban mamaki.
Sannan akwai kuma batun siyasa ta duniya baki daya, wadda ta hangi wasu wurare da suke da ma’adinai, wanda kuma ma’adinan nan suna da matukar amfani sosai, saboda haka dole sai an tashi wadanda suke zaune a wannan wuri ta hanyar tsorata su, sai a kore su daga wannan wuri a kwashi abin da za a kwasa.
Wannan idan ka hada su shi ne ya taso da mu daga yanayin da aka zo ana sace-sacen shanu, aka zo yanayin da babu ma shanun da za a sata, an koma ana tare mutane ana sacewa suna ji suna gani, a wasu lokutan ma har ana shaida wa gwamnati cewa, muna nan zuwa a jira mu. A je makaranta, a zauna a kan titi a gari, a kama mutane a ce sai ka kawo kaza ko kaza, duk wannan binciken mun yi shi mun kuma fadawa mutane cewa, wannan abin yana tawowa, saboda haka ya dace a san abin da za a yi.
Wannan abu bai tsaya iya nan ba, abin da zai ba ka ta’ajibi shi ne za a ce, an kama mutum za a kawo miliyan goma, sai kuma a je a kawo din. Saboda haka, me wannan yake nunawa kenan? Kai tsaye yana tunatar da kai cewa, a kasar nan wasu abubuwa na mulki sun faru, wadanda babu gaskiya a cikinsu, babu kuma rikon amana. Mutane sun talauta gwamnati, sun saci kudin gwamnati har ya kasance in an kama su an ce a ba da kudi za a bayar, tunda aka farad a maganar miliyan daya ko biyu, sai da aka zo ana karbar miliyan dari, abin nan an yi shi ba sau daya ba, ba sau biyu ba, muna da gwamnati amma kamar ba mu da ita, ana ji ana gani ba a daukar wane irin mataki, mun yi maganar wannan abu mun fade shi, ba sau daya ba ko sau biyu ba, har said a yakin ma ya zo ya ci kowa da kowa, yanzu an karbe shi kamar shi ne rayuwa.
Haka aka yi a mulkin Buhari, kowa yana tsammanin cewa Nijeriya za ta samu kwanciyar hankali, Nijeriya ta samu sauki, kowa ya zama yana da kwanciyar hankali, haka nan ya yi shekarunsa hudu na farko abin da ake tsammani ba a samu ba, kuma ana ganin alkawuran ma da ya yi ba su samu ba maganar tsaro, maganar tattalin arziki da kuma batun sama wa matasa aikin yi, haka aka wuce wadannnan shekara hudun, amma sai aka ce a yi hakuri ai yanzu aka fara, to wannan alkawuran haka aka yi ta yin su, yanzu a Nijeriya babu sana’ar da ta fi wannan samu shi ya sa zai wahala a bar ta, domin sai mutum ya sha bakar wahala.
Sannan wadannan barayi, ba za su taba sayen saniya guda daya ba, sai dai ya hada baki da irin wadancan mutanen sai ka gan su da saniyar. Saboda haka, ayyukanmu a wannan cibiya sun shafi wayar da kan al’umma cewa, sai fa an tashi tsaye ne za a iya kawar da irin wannan barna, sannan dole sai an tashi tsaye za a gyara wannan demokuradiyya.
Ma’ana wadanda aka zaba; ba kansu kadai za su rika kallo ba, wajibi ne su rika kallon talakawa domin kuwa babu wanda ya kai su shan wahala, sannan abin da yake bukata kawai shi ne yadda zai samu abin da zai ci, a kuma kyautata masa asibiti da makarantu, ya zamanto cewa yaransa za su iya zuwa makaranta, idan suka kammala kuma su samu abin yi. Domin kuwa, wannan ne ke gina jama’a tare da inganta su, wadannan abubuwa aka nema aka rasa, shi yasa cibiyarmu ta rika jan hankali ta hanyar amfani da gidajen rediyo, jaridu da kuma tarurruka da ake yi a kan cewa, dole fa sai an dawo kan turbar demokuradiyya, an bi hanyar da ta dace idan ana so a samu zaman lafiya.
Wace shawara za ka bai wa shugabaninmu da sauran kasashe, don kauce wa abubuwan da ke faruwa a sauran kasashen da ke makwabtaka da mu?
Ai wato maganar guda daya ce tak, kamar wadda muka fara da ita, ita harkar mulki idan aka ce an tsaya a matsayin kasa, to dole ne a samu shugabanni, domin ba zai yiwu a ce kowa ya zama Shugaba ba, don haka me shugaba ya kamata ya yi? Abin da shugaba ya kamata ya yi shi ne adalci, misali lokacin da wannan sabon shugaba ya zo, yana daya daga cikin abin da mutane ba su kula da shi ba, koda-yake kowa ya sani harkar siyasa an yi amfani da kudi da sauran makamantansu, amma mafi yawan mutane sun zabi Ahmed Bola Tinubu ne da nufin cewa dan siyasa ne, idan ka duba duk zabukan da aka yi a shekarun baya za ka ga jami’an tsaro sun mara masa baya, misali Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Obasanjo, ai soja ne shi ma Umaru Musa ‘Yar’aduwa da Jonathan sun samu goyon bayan Obasanjo, ka ga dai ai duk harkar soja ce da sauransu.
Sannan na ukunsu da ya zo Buhari ne, shi ma kuma soja ne; lokaci daya da muka samu wanda mun san dan siyasa ne wanda an san cewa ya ginu cikin siyasa kuma ya dade yana yin ta, sannan kuma yana daya daga cikin wadanda suka sadaukar da ransu don tabbatar da siyasar a wannan kasa. Wani lokaci ma, har sai da ya gudu ya bar kasar, wannan ne yasa kamar yadda aka yi wa Buhari kyakykyawan zato, shi ma aka yi masa a matsayinsa na mashahurin dan siyasa.
Shi ya sa aka rika tsammanin cewa, tun da ga dan siyasa ya zo za a zo a yi siyasa, amma sai ga shi tun daga zaben ministocinsa, aka gano cewa kwata-kwata ma bai ma yi shirin yin siyasar ba, domin tambayar da aka rika yi masa a lokacin ita ce, har da irin wadancan za ka zabo? To in dai su ne za ka zaba me ya sa har ya dauke ka tsawon watanni ba ka zabo su ba?
Har ila yau, bayan an rantsar da shi a matsayin Shugaban Kasa, maganarsa ta farko ita ce batun cire tallafin man fetur, wanda babu sakarcin da ya wuce wannan. Dalili kuwa shi ne, duk inda ake maganar gabatar da mulki karfafa, ita ce Magana ta farko; bayan nan ne sai aka sa wani abu da zai kawo damuwa gare su, to ba za su ga damuwar ba saboda ka riga ka kafa su, saboda sun samu abin yi to duk abin da Sunusi Lamido Sunusi ke fadi, dama karya ce mu mun sani, saboda dukkaninsu ‘yan baranda ne, yaran turawa. Ga shi nan yanzu an kai mu an baro, an cire tallafin man an ce kudadenmu su kwaci kansu da kansu, to yaushe kudinmu zai kwaci kansa a kasar da ba ta iya kirkirar komai nata na kanta? Idan aka ce za abi wancan tsarin, sai idan kasarka na iya kirkirar wani abu na cinikaiya, wanda za a zo a saya.
Ko kana da wata shawara da za ka bai wa talaka ganin cewa, kusan duk abin a kansa yake karewa?
Sosai ma kuwa, amma ka san duk maganar da ake yi na mulkin jama’a ne, amma tsakani da Allah shi talaka me yake bukata a rayuwarsa? Wani lokaci Buhari ya ce, talakan Nijeriya malalaci ne; bincike ya nuna mana wannan magana ba ta da tushe ko kadan. Misali, ka bi manyan tituna za ka ga mutane na hakan lambatu, domin sanya waya na kamfanin sadarwa, su wane ne ke yin irin wadannan ayyuka idan ba talakawa ba? Don haka, Talakan Nijeriya ba rago ba ne, ba kuma cima zaune ba ne.
Abin da talaka yake bukata bai wuce kula da shi ba, wallahi ko gidanka ba zai rika zuwa ba, idan ya san cewa in ba shi da lafiya akwai asibitin da zai je, in kuma ya je zai samu magani. Haka nan, idan yaronsa ya isa zuwa makaranta, ba sai ya wahala ba, yaron nan kuma za a karbe shi a kula da shi a harkar makarantar, in yaro ya gama makaranta kuma zai samu aikin yi.
Haka zalika, abin da ake bukata shi ne a bunkasa harkar noma, kamar yadda aka yi a da. A kuma baiwa mutane karfin gwiwa su fita su yi noman, a samar da taki isasshe a kuma arha tare da sauran kayan aikin noma. Sannan, a je a kyautata wa kasuwa, a tabbatar da farashin abubuwa ba su canza ba, wanda kuma ya kasance Manomi ne a samar masa da kayan nomansa da sauran makamantansu.