Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Da Aka Gudanar A Amurka Ta Nuna Damuwa Kan Makomar Tsarin Demokiradiyar Kasar

Daga CRI Hausa

Rahotanni na cewa, sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka kada a Amurka, ya nuna cewa, tasirin demokiradiyar kasar, yana cike da matukar damuwa.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa kan wadannan rahotanni, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi nuni da cewa, Amurka tana da tarin matsaloli, kana ba ta cancanci ta rika irin wannan girman kai da nuna bambanci na tilastawa da nuna isa ba. Har ma ta ke neman kakabawa sauran kasashe tsarin demokiradiyarta.

Zhao Lijian, ya bayyana cewa, alakar Sin da Amurka tana fuskantar zabi na hanyar da za ta daso.

Ra’ayin kasar Sin a bayyana yake.

A don haka, ya kamata sassan biyu su zabi hanyar cudanya cikin lumana, da tsarin hadin gwiwa da moriyar juna tsakanin manyan kasashe masu bambacin tsare-tsare da na al’adu da bambancin matsayi na ci gaba ta hanyar tattaunawa. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

Exit mobile version