Kwalejin Koyar da Digiri na Biyu (PGC) ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ta gudanar da bikin ƙaddamar da sabbin ɗalibai na shekarar karatu ta 2023/2024. An yi taron ne a babban ɗakin taro na jami’ar da ke Zariya tare da halartar shugabanni daga jami’a da baƙi daga sassa daban-daban.
Shugaban kwalejin, Farfesa Mohammed Nasir Shuaibu, ya ce wannan bikin yana tabbatar da cika sharuɗɗan shiga jami’ar, yana mai kira ga ɗalibai da su kasance masu ladabi da gaskiya a neman ilimi tare da nisantar aikata laifuka kamar satar jarrabawa da shiga ƙungiyoyin asiri.
- Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Duba Dalili
- Taron Matasan Sin Da Afrika Kan Tsaro Zai Kirkiro Wata Sabuwar Mahanga Ta Magance Matsalolin Tsaro
Bincike ya nuna cewa cikin ɗalibai 6,953 da suka nemi gurbin karatu, an amince da 5,384, ciki har da masu PhD 725, Masters 2,558, PGD 371, da ɗalibai 145 daga ƙasashen waje. Farfesa Adamu Ahmed, muƙaddashin shugaban jami’ar, ya jaddada cewa jami’ar ta kafa tsarin lura da ɗalibai domin tabbatar da kammala karatu cikin lokaci da inganci.
Wasu sabbin ɗalibai sun roƙi gwamnati da jami’a su duba halin tattalin arziƙi wajen sassauta kuɗin makaranta. Bikin ya gudana lafiya kuma ɗalibai da dama sun bayyana fatan kammala karatu cikin nasara da salama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp