Kwamitin Majalisar Wakilai kan sake kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasa ya ba da tabbacin samar da ingatacce kundin tsarin mulkin kasa da zai inganta ya kuma shigo da kowa da kowa da ke tattare da muradi da burin ‘yan Nijeriya nan da watanni 24 masu zuwa.
Shugaban kwamitin majalisar, Benjami Okezie Kalu, shi ne ya shaida hakan a lokacin kaddamar da kwamitin.
- Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Kar-ta-kwana Kan Haramtattun Gine-gine
- An Halaka Mutane A Chadi Bayan Yunkurin Kashe Shugaban Kotun Koli
Ya ce, daga cikin bangarorin da gyaran kundin tsari zai maida hankali da suka zo sakamakon kudurorin da majalisar ta amsa sun hada da kudurin kafa ‘yansandan jihohi, bai wa jihohi ikon samun dama kan ma’adinai, samar da karin damarmakin shigowar mata cikin harkokin siyasa, fayyacce ko bayanannen harajin da kowace gwamnati za ta amsa, da kuma tanadi ga ofishin magajin birnin tarayya Abuja.
Kalu ya kuma kara da cewa akwai wasu kuduriron doka da za su tsallake ba tare da sanya hannu da amincewar shugaban kasa ba a lokacin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki karo na biyar, don haka an dawo da su yanzu za a sake yin bita kansu domin yin abubuwan da suka dace.
Ya kara da cewa, “A shirye kwamitin nan yake wajen amsar wasu karin kudurori domin kyautata tsarin mulkin kasa wajen bunkasa dimukuradiyyarmu.”
A nasa bangaren, kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ba da tabbacin cewa sabon kundin tsarin mulkin zai kasance mai shigo da kowani bangare tare da wanzar da gaskiya da adalci daidai da bukatun ‘yan Nijeriya.