Daga Rabiu Ali Indabawa,
Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantun sakandare 10 da ke ba da tallafi na wucin gadi a Ilorin, babban birnin jihar, har sai an shawo kan rikicin Hijaab a makarantun da abin ya shafa. Makarantun sune; Kwalejin C & S, ST. Anthony College, ECWA School, Surulere Baptist Secondary School, Bishop Smith Secondary School, CAC Secondary School, St. Barnabas Secondary School, St. John School, St. Williams Secondary School da St. James Secondary School duk a cikin garin Ilorin.
Wasu daga cikin makarantun, a ranar Juma’a ana zargin sun kulle wasu daliban sanye da hijabi. A ranar Larabar da ta gabata, wasu kungiyoyin Musulmai sun bukaci gwamnatin jihar da ta nuna wa mahukuntan makarantun da abin ya shafa damar barin dalibansu mata sanya hijabi. Wannan ya sanya ganawa tsakanin gwamnatin da shugabannin Kiristoci da Musulmai a jihar ranar Alhamis.
A taron wanda Mataimakin Gwamna Kayode Alabi ya jagoranta, jihar ya bukaci dukkan bangarorin da su binne bambance-bambancen da ke tsakaninsu su kuma bar zaman lafiya ya ci gabawanzuwa.
“Za a ci gaba da sadarwa don sanar da mambobi ga ci gaban. “Gwamnati ya yi kira da a kwantar da hankula tare da yin kira ga iyaye da shugabannin addinai da su guji aiki ko kalaman da ka iya kara raba kan al’ummomin biyu.