Farfesa a fannin harkokin banki da hada-hadar kudi na jami’ar Cardiff a kasar Burtaniya, Kent Matthews ya bayyana cewa, kasar Sin tana kan hanyar zama kasa ta farko a duniya, wajen yin hada-hada ba tare da tsabar kudi ba. Masanin ya bayyana haka ne, kwanakin baya yayin wata hira ta musamman da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua.
Mattthews ya bayyana cewa, adadin tsabar kudaden dake yawo a hannun jama’a a kasar Sin, ya ragu zuwa kashi 3.7, kuma yana ci gaba da raguwa sannu a hankali. A cewarsa yanzu haka ba sosai mutane suke amfani da tsabar kudi ba, kan yadda lamarin yake shekaru 10 ko 20 da suka wuce, kuma tsarin yana kara samun karbuwa a tsakanin al’umma. Yana mai cewa, yau a Biritaniya tsabar kudaden dake yawo a hannun jama’a, ya kusa kai kashi 2.9 cikin 100 na adadin kudaden dake kewayawa a cikin al’umma.
Ya ce, a cikin kasa da shekaru 20, kasar Sin ta cike gibin da ke tsakaninta da Burtaniya ta fuskar rashin amfani da tsabar kudi a tsakanin al’umma.
A cewarsa, wannan ya nuna yadda hada-hadar kudi ta hanyar fasahar zamani ke saurin bunkasa a kasar Sin, da ma yadda al’ummar kasar suka karbe shi cikin sauri. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)