A ranar Laraba 22 ga watan Yuni 2022 Kamfanin LEADERSHIP ya cika shekara daya da fara gabatar da shirye-shirye ta hanyar manhajar PODCAST daga dakin watsa shiriye-shirye na zamani na LAST WORD a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya.
Mahukuntan kamfanin LEADRSHIP sun yi alkawarin kara inganta ayyukan bangaren don jagorantar kafafen watsa labarai na kasar nan a fannin yada labarai ta hanyoyi na zamani, musamman ganin yadda al’umma ke kishi da fatan samun sahihan labarai.
Da yake tsokaci a kan cikar sashin shekara daya da kafuwa, shugaban shashen yada labarai na Kamfanin LEADERSHIP, Mista Bayo Amodu, ya ce, “shirye-shiryenmu na Podcast sun samar da mahanga ta musamman a tsarin gabatar da shirye-shirye ta kafafen sadarwa na zamani tun da aka kafa ta, don haka muna yi wa masu bibiyarmu alkawarin inganta yadda ake gabatar da shirye-shirye don samar musu da hirye-shirye masu kayatarwa, ilimantarwa da fadakarwa a cikin shekaru masu zuwa.
“A ranar Laraba 22 ga watan Yuni 2022, aka fara gabatar da shirye-shirye daga dakin watsa shirye-shiryenmu na Podcast.
Dalilan fara shirin ta hanyar wannan tsari shi ne yadda muka lura da cewa, bangaren gabatar da shirye-shirye ta kafafen sadarwa na zamani babu kwararrun ‘yan jarida a ciki, galibin masu yi suna kiran kansu da sunaye iri iri, ba sa yin cikakken bincike wajen gabatar da labarunsu, ta haka kuma suke watsa labarai marasa inganci ga al’umma.
“Ina sane da wurare daban-daban da labarun kanzon kurege suka haifar da matsaloli ga al’ummar Nijeriya da dama. Amma mu a Kamfanin LEADERSHIP an san mu da samar da ingattun labarai, mun kuma dade a fagen harkar watsa labarai a kan haka muka shigo don cike gurbin da al’umma ke bukata a fagen watsa labarai ta kafafen sadarwa na zamani.
“Mun yi gaggarumin kokari a cikin shekarar da ta wuce. Mun samar da tsari na musamman a bangaren aikin jarida ta kafafen sadarwa na zamani, yawan mutane da ke bibiyarmu da kuma sakonnin da muke samu a kullum shaida ne ga yada aka karbe mu, yana kuma nuna irin kokarinmu a wannan fagen.
“Mun samar da shirye-shirye da dama, muna ci gaba da inganta su tare da tsayuwa a kan bayar da sahihan labarai. Za mu nisanci dukkan nau’in labarun kazon kurege, za kuma mu tabbatar da kowa ya samu hakkin fadar albarkacin bakinsa a dukkan lokaci,” in ji shi.
Mista Amodu ya kuma bayana cewa, bayan shirye-shirye ta Podcast, Kamfanin LEADERSHIP Group Limited, na kuma jagorantar buga Jaridar LEADERSHIP Daily, LEADERSHIP Weekend, LEADERSHIP Sunday, LEADERSHIP Hausa da kuma National Economy.
Daga cikin manya manyan shirye shiryen da ake gabatarwa a dakin watsa shirye-shiryen na LAST WORD akwai shirin sashashin Hausa na LEADERSHIP mai lakabin ‘BARKA DA HANTSI NIJERIYA’ wanda ake gabatarwa da misalin karfe 9 na safe daga Litinin har zuwa Juma’a kai-tsaye ta kafofin Facebook a “Leadership Hausa”, YouTube a “Leadership Hausa”, sai kafar Twitter a “@Leadershiphausa”.