Kungiyar likitocin Nijeriya (NARD) ta bayyana cewa yawan likitocin kasar nan suna raguwa a kullun, inda ta ce a halin yanzu likitoci 10,000 kacal suka rage.
Shugaban kungiyar NARD, Dakta Emeka Orji shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata.
- Celestine Babayaro Ya Sake Bayyana Bayan Ya Bace
- Buhari Ne Ya Jefa ‘Yan Nijeriya Cikin Kangin Talauci — Gwamnoni
A cewar Orji, sama da likitoci 100 suke barin kasar a duk wata wajen neman aiki mai kwabi a kasashen ketare.
Ya ce, “Na sani a halin yanzu muna da likitoci 24,000 ciki har da kwararu da likitocin gida da sauran ma’aikatan lafiya. A cikin likitoci 80,000 da aka yi wa rajista, kashi 64 ba sa gudanar da aikin, wasu sun fice daga kasar, yayin da wasu sun yi ritaya, wasu sun sauya aiki, wasu kuma sun mutu.
“Likitocin gida da muke amfani da su guda 16,000 a baya, amma a yanzu muna da 9,000 zuwa 10,000. Ba za mu iya tatance yawan likitocin ba a kullum, saboda ficewa da suke yi. Saboda haka, a yanzu haka muna da likitoci a tsakanin 9,000 zuwa 10,000 a fadin kasar nan.
“A jimlace, muna da likitoci 24,000 ciki har da kwararu da likitocin gida da ma’aikatan lafiya. Kungiyar kula da lafiya ta duniya ta bayar da shawarar cewa ilita daya ya dunga duba majinya ta 600, amma a halin yanzu a Nijeriya, likita daya yana duba marasa lafiya guda 10,000.”
Shugaban NARD ya kara da cewa babban matsalar da ta kawo ficewar likitocin shi ne, rashin ba su hakkokinsu da rashin samun walwala da kuma rashin tsarin samar da gidajensu.
“Muna fuskantar rashin kyawun yanayin wurin aiki a kasar nan, idan gwamnati tana son ma’aikata su gudanar da aiki yadda ya kamata, to dole ne ta inganta wuraren aiki. Idan ana bukatar bangaren lafiya ya kasance da ransa, to dole kowa ya saka hannu cikin lamarin.
“A wannan shekarar tsakanin watannin Janairu zuwa Agusta, mun rasa sama da likitoci 800, lokacin da muka tambaye su dalilin ficewarsu, kashi 80 sun bayyana cewa saboda rashin biyansu hakkokinsu da kuma rashin kyawon wurin zama,” in ji Orji.