CRI Hausa" />

Lokaci Ya Yi Da Mike Pompeo Ya Dakatar Da Abubuwan Da Yake yi A Baya

Kwanan baya, jaridar The Washington Post ta kasar Amurka, ta fitar da wani sharhi, inda a cikinsa aka yi tir da suka mai yawa kan sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo. Hakan dai ya biyo bayan abubuwan da ya yi, bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, lamarin da ya sanya shi zama a matsayin daya daga cikin mafiya rashin kwarewar aiki a jerin sakatarorin wajen da Amurka ta taba yi a tarihi.

Bayan barkewar annobar, kila Mike Pompeo ya hangi damar shafa wa kasar Sin kashin kaji, da sunan barkewar annobar bisa ra’ayin yakin cacar baki, yana kallon duniya da tunaninsa. Abun da ya yi ya girgiza kasashen duniya, kana kwararru na Amurka su ma sun yi ta sukar sa.
Susan Rice, tsohuwar mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasar Amurka, ta soki Pompeo cikin wani shirin rediyo a kwanan baya, inda ta ce, kalaman Pompeo dangane da annobar “cutar Wuhan”, babban abun kunya ne ga Amurka.
A ’yan kwanakin baya, tsoffin manyan jami’an gwamnatin Amurka, da kwararrun kasar kusan dari daya, sun aika da wata wasika a fili mai taken “a kubutar da rayuka a kasashen Amurka, Sin da ma duk duniya baki daya”, inda suka yi kira ga kasashen Sin da Amurka, da su hada kai wajen kandagarki da dakile yaduwar annobar ta COVID-19. A cikin irin wannan hali ne ya kamata, ko wane dan siyasan Amurka mai sauke nauyi kuma mai sanin ya kamata, ya yi kokarin kara nema wa Amurkawa taimakon kasa da kasa, da kara azama kan hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar.


Amma Pompeo ya ci gaba da yin karya, ya ci gaba da shafa wa kasar Sin kashin kaji, a yunkurin samun ribar siyasa. Bai kula da rayukan jama’ar Amurka ba, bai kula da moriyarsu ba, kuma ya kawo cikas wajen yaki da annobar cikin hadin gwiwar kasa da kasa.
Ana dai kallon Pompeo a matsayin daya daga cikin mafi rashin kwarewa a jerin sakatarorin wajen da Amurka ta taba yi a tarihi, kuma lokaci ya yi da ya dakatar da abubuwan da yake yi a baya. Kowa na kara fahimtar cewa, sha’anin da yake himmantuwa a kai, ba zai kawo wa Amurka komai ba, sai abun kunya da rashin sa’a. (Mai Fassarawa: Tasallah Yuan)

Exit mobile version