Ma’aikatan shari’a a Jihar Kogi ƙarƙashin ƙungiyar JUSUN sun shiga yajin aikin sai baba ta gani sakamakon gazar gwamnati na cika alƙawarin biyan bashin watan Oktoba 2024 da kuɗin hutun shekarar 2025. A cikin sanarwar da shugaban JUSUN, Emmanuel Waniko, da sakatare, Sule Suberu, suka fitar, ƙungiyar ta ce an shiga yajin aikin ne bayan jinkirin da gwamnati ta yi duk da alkawurran da ta ɗauka tun lokacin da aka dakatar da wani yajin aikin da ya gabata.
JUSUN ta bayyana cewa Gwamna Usman Ododo ya tabbatar da amincewa da biyan kuɗaɗen, amma ba a ga wani mataki ba na aiwatar da hakan duk da haƙurin da ma’aikata suka nuna. Kungiyar ta ce dole ne ta ɗauki wannan mataki domin kare muradun membobinta da ke fama da matsin tattalin arziki sakamakon biyan da ya tsaya.
- Mutum 4 Sun Mutu Yayin Da ’Yan Bindiga Sake Kai Hari Kogi
- Gwamnatin Kogi Ta Ƙaryata Rahoton Sace Ɗalibai A Jiharta
Sanarwar ta bayyana cewa daga ranar Alhamis, 4 ga Disamba 2025, dukkan ma’aikatan shari’a a jihar su dakatar da aiki gaba ɗaya, tare da gargadin cewa ba a yarda wani ya shiga ko ya gudanar da wani aiki na hukuma ba har sai an biya kuɗaɗen da ake binsu. Ƙungiyar ta jaddada cewa har sai an biya bashin watan Oktoba 2024 da kuɗin hutun 2025, babu komawa bakin aiki.
JUSUN ta yabawa membobinta bisa jajircewa da haɗin kai, sannan ta bukaci su ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen ganin an biya haƙƙinsu. A halin yanzu dai sashen shari’a na jihar ya tsaya cik, lamarin da ka iya kawo tsaiko ga ayyukan kotuna idan gwamnati ba ta gaggauta ɗaukar mataki ba.














