Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

MACBAN Ta Soki Gwamnatoci Bisa Rashin Ware Wa Makiyaya Kaso A Kasafi

by Muhammad
December 29, 2020
in RIGAR 'YANCI
3 min read
MACBAN
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya,

 

samndaads

Kungiyar Fulani ta MACBAN ta ce rashin ware wani kaso a cikin kasafin kudin gwamnatoci domin kula da rayuwar Makiyaya a fadin kasar nan abun damuwa ne, su na masu cewa irin dumbin yawa da muhimmancin al’ummomin Fulani sun dace ake ware kaso na musamman domin su.

Sun kuma bukaci gwamnatoci a dukkanin matakai da su dauki dukkanin matakan da suka dace wajen ganin sun taimaka wa Makiyaya a fadin kasar nan lura da yadda su ma suke kokarin samar wa gwamnati kudaden shiga.

Ahmad, ya jawo hankalin gwamnatoci da su ke kula da maida hankali kan Makiyaya duk lokacin da suke fitar da kasafin kudi na shekara-shekara domin inganta wa Fulani rayuwarsu.

Sadik ya lura da cewa dukkanin alkawuran da aka yi ta yi wa Makiyaya a fadin kasar nan a baya har zuwa yanzu an kasa cimmawa illa kawai ana zanawa a takarda ba tare da aiwatarwa ba.

Ya shawarci gwamnatoci da suke jawo shugabannin Fulani wajen fitar da tsare-tsare da shirye-shirye domin tabbatar da al’ummominsu sun amfana daga shirye-shiryen gwamnati a kowani lokaci.

Kwamared Sadik ya kuma bukaci jama’a da jami’an gwamnati da su daina kallon Fulani a matsayin ‘yan ta’adda, ya na mai cewa tarihin kasar nan ba zai taba mance da kyakkyawar tarihin al’ummar Fulani ba, inda ke cewa daina kallon Fulani a matsayin ‘yan ta’adda zai kare musu kima da mutunci a kasa da ma duniya baki daya.

Shugaban MACBAN na jihar Bauchi ya lura kan cewa sabon jagorancin MACBAN a fadin kasar nan yanzu haka ya dauki alkibla gami da cewa jihar Bauchi ta kasance na gaba-gaba wajen fitar da tsare-tsare masu kyawu, a cewarsa ta wannan kyakkyawar salon shugabanci da jagoranci da aka sanya a gaba yanzu, zai kai ga shawo kan matsalolin da suke akwai gami da inganta wa Fulani rayuwarsu.

Ya nemi shugabanin Fulani a dukkanin matakai da su tashi tsaye wajen ganin sun kara himma da kokari wajen kyautata rayuwar Makiyaya da nema musu muhimman ababen more rayuwa.

Kwamared Sadik Ibrahim ya na mai cewa a halin yanzu MACBAN tana matukar bukatar jagorori tsayayyu wadanda za su ke fitowa domin daukaka sautin al’ummarsu da suke da tulin bukatu a dukkanin matakai.

Shugaban na MACBAN ya alakanta rikice-rikicen da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya na faruwa ne a sakamakon rashin adalci gwamnatoci na gaza tabbatar da hanyar kiwo (Labi) da kuma wuraren shan ruwan dabbobi na musamman da aka ware domin makiyayi da dabbobininsa a fadin kasar nan.

Sai ya ke bada tabbacin cewar a karkashin sanya idonsa da kulawarsa zai yi iya kokari wajen ganin makiyaya a fadin jihar Bauchi sun samu rayuwa mai inganci, ababen more rayuwa, ilimi da sauran fannonin da za su kyautata rayuwarsu.

Ya nemi hadin kan Fulani domin cimma nasarorin da ya sanya a gaba, tare da fatan gwamnatoci za su ji korafe-korafensu na ganin sun shigar da Fulani cikin harkokin more rayuwa.

Da ya ke jinjinawa tare da yaba wa salon shugabanan MACBAN a jihar Bauchi, shugaban kungiyar a shiyyar Bauchi ta kudu, Alhaji Adamu A. Musa Sarkin Ginzum, ya shaida cewar salon jagorancin MACBAN a jihar Bauchi a daidai wannan lokacin sai sambarka domin an dauko hanyoyin kyautata rayuwar Makiyaye a dukkanin matakai.

SendShareTweetShare
Previous Post

Sace Daliban Kankara: Wasan Kwaikwayo Gwamnatin Katsina Ta Shirya, Cewar Mahdi Shehu

Next Post

’Yan Bindiga Sun Kashe Biyu, Sun Yi Garkuwa Da 48 A Katsina

RelatedPosts

Ingantaccen zabe

Aniyar Ganduje Ce Ta Haifar Da Ingantaccen Zabe A Kano – Yusif Ali

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, An bayyana cewa, kyakkyawar aniyar Gwamna...

Kaduna

Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Bindiga Kwanton Bauna A Kaduna

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Sojojin da ke karkashin ‘Operation Thunder...

Farar Hula

Hankula Sun Tashi A Maiduguri Bayan Babbaka Sojan Da Ya Harbi Farar Hula Hudu

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Mutanen Maiduguri sun shiga tararrabi bayan...

Next Post
Bindiga

’Yan Bindiga Sun Kashe Biyu, Sun Yi Garkuwa Da 48 A Katsina

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version