Mace Ta zama Ministan Tsaro A Indiya

Tare da Sani Anwar 08036365416 (leadershipayau.com)

An nada mace a matsayin ministan tsaro a kasar India, Hakan ko ya biyo bayan garanbawul ne da Firayiministan Ministan kasar Nerendra Modi yayi wa majilisar gudanarwansa.

Jiya Lahadi Firaministan Indiya Narendra Modi ya nada wata mace a matsayin Ministar Tsaro, bayan da ya yi garanbawul ma Majalisar Ministocinsa, a wani yinkuri na cike wasu muhimman alkawurra da ya yi tun kafin babban zabe da za a yi nan da shekara daya da rabi.

Nirmala Sitharaman za ta zama mace ta farko a wannan matsayin tun bayan shekaru 35, lokacin da tsohuwar Firaministar Indiya Indira Ghandi ta zama Ministar Ma’aikatar ta tsaro ita ma.

Sitharaman, ‘yar shekaru 58 da haihuwa kuma tsohuwar karamar Minista a Ma’aikatar Kudi, ta hau wannan mukamin ne a daidai lokacin da takaddama tsakanin Indiya da makwabtanta biyu da ke sashin arewa, wato China da Pakistan ke dada tsanani. Ana yaba mata saboda karfin hali da kwarewa da kuma hazaka.

Ita ce mace ta biyu kan babban mukami a Majalisar Ministocin, Sushma Swaraj ita ce Ministar Harkokin Wajen kasar.

Modi ya nada sabbin ministoci 9 a yayin da ya ke mai da hankali kan gudanar da shugabanci na gari a tsawon shekara daya da rabi da ya rage a wa’adinsa.

               

 

Exit mobile version