Daga Abubakar Abba, Kaduna
Wani ɓangare na magoya bayan jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, da aka fi sani da APC Aƙida, sun buƙaci Majalisar Ƙasa, da ta yi watsi da buƙatar da Gwaman Jihar Malam Nasir Ahmed el-Rufai ya tura mata na son ciwo bashin Dalar Amurka Miliyan 350.
Buƙatar na ƙunshe ne a cikin wasiƙar da suka rubutawa Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da basussukan ƙasar waje da cikin gida, wanda kuma aka raba wa manema labarai.
Wasiƙar ta ce, “a matsayinmu na ‘yan jiha, ya zamar mana wajibi mu rubuta wannan wasiƙar, don janyo hankalin Majalisa, idan aka yi la’akari da yunƙurin Gwamna el-Rufai na son jinginar da jiha ta hanyar ciwo wannan bashin, wanda in an ciwo shi, a ƙarshe ba zai haifarwa da jiha ko ‘yan jiha ɗa mai ido ba, musamman idan aka yi la’akari da ɗimbin kuɗin ruwan da ke tattare da bashin.”
Har ila yau sun yi nuni da cewar, “idan aka waiwaya baya, sakamakon karɓar da Majalisar Ƙasa ta yi, ranar 1 ga watan Yuni na shekarar 2017 na ciwo bashi daga ƙasar waje daga Fadar Shugaban Ƙasa, a madadin jihohi har da jihar da ta rubuta tana son karɓar bashin Dalar Amurka Miliyan 350, wanda ya yi daidai da Naira Biliyan 122 da nufin zuba bashin a cikin tsare-tsaren gwamnatin jihar, tun lokacin da gwamnatin ta nuna wannan niyyar tata, al’ummar jihar suke ta nuna damuwarsu akan son ciwo wannan bashin, musamman idan aka yi la’akari da yadda ɗimbin basussuka suke ƙara yiwa jiha yawa.
Sun ƙara da cewa, “Gwamna el-rufai bai ƙirƙiro da wasu ayyuka da za su inganta rayuwar ‘yan jiha ba kuma gwamnatinsa, ba ta bin ƙa’ida a kan yadda take gudanar da ayyukan gwamnati, saboda haka bai dace a ƙara tilastawa jiha wani sabon bashi ba.
Haka zalika sun ce a yanzu ɗimbin bashin da ake bin jihar daga ranar 30 watan Mayu na shekarar 2015, ya kai jimlar kimanin Naira Biliyan 74.
Sun bayyana cewar akwai buƙatar a daddale menene alfanun da ciwo bashin ke da shi ga ‘yan jiha da kuma ta wacce hanya za a bi don biyan wannan bashi in an ciwo.
Sun yi nuni da cewa, ‘yan jiha Kaduna suna da ‘yancin su tofa albarkacin bakinsu akan wannan bashin da gwamnatin jiha ke son ciwo wa, ta hanyar amincewa dashi ko ƙin amincewa dashi.
A cewarsu, “muna son mu yi tambaya, shin wane abu ne ‘yan Kaduna suka fi so? Idan har dama dimokiraɗiyya an yi ta ne don zaɓin abinda jama’a suke so, to, alummar jiha Kaduna suna da hakkin su gayawa gwamnati gaskiya domin da bazarsu ce ake rawa.”
Sai dai, sun bayyana cewa, gwamnati tana jin tsaoron ta kira taron masu ruwa da tsaki akan maganar domin tasan in ta kirawo, a ƙarshe za ta fuskanci fushin jama’a ne da kushewa.
Sun bayyana cewar, “kowa yau ya sani jiha Kaduna ita ce ta biyu wajen ɗimbin bashin da ake binta a ƙasar nan, kuma duk da haka ba wani abin a zo a gani da aka tsinanawa al’ummar jiha.
APC Aƙida sun zargin an yi almubazzarantar da da kuɗin Paris Club da aka bada da kuma wasu kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ta tallafawa jihohi na agaji da ake yiwa laƙabi da (bailout), waɗanda wannan tallafin an bayar da su ne don gudanar da wasu manyan ayyuka da suka haɗa da biyan albashin ma’aikata.
Haka zalika sun koka matuƙa kan yadda aka samu malaman makaranta a jihar su kusan 25,000 gwamnati ta kasa biyansu albashinsu da ya kai na kusan Naira Biliyan 2.3.
Sun yi zargin cewa, gwamnatin ta el-Rufai ba ta bin ƙa’ida wajen wajen gudanar da harkar shugabanci da kuma ƙaddamar da ayyukan a jiha da bada kwangiloli, inda hakan ya janyo ƙwangilolin da ta ƙirƙiro da su ta kasa kammala su.
A ƙarshe APC Aƙida ta ce, ciwo bashin kan iay gadar da talauci hatta ga ‘ya’yan jihar da su zo duniya ba.