Magoya bayan jam’iyyar PDP a Jihar Ribas, sun gudanar da zanga-zanga a garin Fatakwal tare da boka don nuna kin goyon bayansu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Masu zanga-zangar na dauke da kayan tsibbu, wanda wannan ita ranar su ta biyu da suke rajin INEC ta ba su damar duba kayayyakin zaben da aka yi amfani da su a jihar.
- Buhari Ya Cika Alkawarin Da Ya Dauka Game Da Zaben 2023 -Gwamnatin Tarayya
- ‘Yan Siyasa Ne ke Kokarin Raba Kan ‘Yan Nijeriya —Solomon Dalong
A ranar Litinin sun kai wa dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar, Tonye Cole hari a yayin da suka yi arangama a hanyarsu ta zuwa ofishin INEC.
A ranar Talata bayan dawowarsu bakin zanga-zangar an hangi shugaban karamar hukumar Ikwerre, Samuel Nwanosike sanye da farin kaya da hula dauke da wasu kayan tsafi, yana furta wasu kalamai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp