Connect with us

MANYAN LABARAI

Mahangar ‘Yan Nijeriya A Kan Bikin Yau Ranar Dimukradiyya  

Published

on

  • Gwamnati Ta Kara Himma A Kan Jan Aikin Da Ke Gabanta – Jabi

 

A daidaita lokacin da gwamnati ke ikirarin samun nasara a kan ayyukan raya kasa, musamman dan murnar ranar dimukuradiyya a kasar nan. Sakataren kungiyar direbobi masu motocin haya na kansu (RETEAN) kuma daraktan tsare-tsare na International Institute Of Professional Security, Kwamred Abdullahi Muhammed Jabi, ya bayyana cewar kanbama ayyukan da gwamnati mai ci ke cewa ta yi a kasar nan ya fi aikin yawa.

Kwamred Jabi ya cigaba da cewar maimakon gwamnati ta yi ta yekuwa a kafafen yada labarai ta mayar da hankali a kan ayyukan raya kasa, kamata ya yi ta bari jama’a su fito su bayyana ayyukan da kansu.

Acewarsa, maganar aikin hanya, ba wata hanyar da aka fara aka kammala har yanzu, balle noman da ake ikirarin yi wanda masu dauke da makamai kusan duk sun daidaita dazukan da manoman ke nomawa.

“Wannan ranar da ake ikirarinta ta dimukuradiyya a kasar nan ta zo mana da yanayin da ba mu yi tsammani ba, musamman yadda annobar Korona ta jefa tattalin arzikin kasar nan a wani yanayin da talakawa ke ji a jikinsu, ya kamata bayan daukar matakan dakile ta da gwamnatin ke dauka ya kamata ta kara kaimi wajen ganin jama’a sun samu sassauci a halin da suke ciki domin kasa ba za ta samu cigaba yadda ya kamata ba dole sai jama’ar ta cikin walwala.

“Tabbas, akwai matsaloli da dama a gaban gwamnati, kuma kudade ba sa shigowa a hannun gwamnati yadda ya kamata, ya zama wajibi ta lalubo hanyoyin samun kudaden shiga ba tare da an takurawa talakawa ba. Muna bukatar ingantaccen tsaro, muna bukatar inganta kasuwanci da ilimi ta yadda kowani dan kasa zai mori mulkin dimukuradiyya. Amma a irin wannan halin da muke ciki yau, talakawa na neman abin sawa bakin salati, kuma ba su da yanayin da zasu samu damar mike kafa dan neman madogara a rayuwa akwai bukatar dubawa.

“Ina kiran shugabanninmu musamman ‘yan siyasa da su sani ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya, da su yi anfani da lokacin su wajen ganin sun fidda al’umma da kasar cikin wannan halin da ta ke ciki. Muna fatan idan shugabanni sun kyautata niyyar su, Allah zai ba su kwarin guiwa, a baya an yi ta yekuwar yin ayyukan raya kasa amma kuma sai ka ga an kasa, amma yanzu bisa zato muna masu fatar Allah ya mayar da tunaninsu akan wannan amanar da ya ba su, ta yadda zasu gina abubuwa masu alfanu a kasar nan, kamar yadda na fadi suna da sauran lokaci a gaban su, idan sun samu mashawarta na kwarai ina da tabbacin zasu iya cin ma gaci domin jama’a ba jam’iyya ne a gaban su babban abinda ‘Yan Nijeriya ke bukata shi ne samun shugabanci na gaskiya da amana ta haka ne kawai kasar nan za ta iya bugun gaba da wannan tsarin na dimukuradiyya,” in ji shi.
Advertisement

labarai