Hussaini Baba" />

Mahara Sun Kashe Mutum 13 Da Garkuwa Da Hakimi Da Matarsa A Zamfara

A yanzu haka mahara na ci gaban da kashe mutane a Zamfara, musamman yankin karamar hukumar Anka. Domin kuwa ko a jiya sun yi wa kauyen Kawaye dirara mikiya, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi. Sun kashe mutum goma sha uku, kuma su kai awon gaba da hakimin Bagega da matarsa.
Wadannan mahara sun dade suna cin-karensu ba babaka, a fadin jihar ta Zamfara duk kuwa da karin sojojin kasa da na sama da kuma shawagin giragen sama, amma bai hana su ci gaba da kashe mutane ne da garkuwa da su ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ASP Shehu Muhammad ya tabbatar da cewa ‘mutum goma sha daya ne suka mutu, kuma yanzu haka rundunar na iyaka kokarinta na dawo da tsaro a garin kuma ta tura karin jam’anta don kara karfafa tsaro.

Exit mobile version