A safiyar ranar Litinin wasu ‘yan bindiga suka kai hari hedikwatar karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutum daya tare da yin awon gaba da wasu bakwai.
LEADERSHIP ta rawaito cewa a makon da ya gabata ‘yan bindigar sun kai hari a ofishin ‘yan sanda na Bungudu inda suka kashe dan sanda daya.
- ‘Yan Bindiga Sun Karbe Ikon Kauyuka 400 A Zamfara -Masani
- ‘Yansanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Masallacin Juma’a A Zamfara
Wani mazaunin garin Bungudu mai suna, Ishaq Bungudu, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun afkawa garin da muggan makamai inda suka yi ta harbe-harbe tare da kashe wani mutum.
Kamar yadda ya shaida, ya ce, an yi garkuwa da wasu mutane bakwai da suka hada da dan Sarkin Bungudu, Abdulrahman Hassan, da kuma tsohon jami’in tsare-tsare na asusun bunkasa noma na kasa da kasa (IFAD), Abubakar S/Fada Bungudu.
Ishaq ya koka kan yawaitar hare-haren da ‘yan bindiga suka kai hedikwatar karamar hukumar a tsukin nan, duk da cewa ita ce karamar hukuma mafi kusa da Gusau babban birnin jihar.
Ishaq ya bukaci gwamnan jihar, Dauda Lawal, da ya yi kokarin magance kalubalen rashin tsaro da ya addabi jihar.
“Kusan kullum ana kai mana hari, duk da cewa muna kusa da Gusau babban birnin jihar, ba mu san me ke faruwa ba, gwamnati ba ta cewa komai, shi (gwamna) ma ba shi da mai taimaka wa harkar tsaro tun da aka rantsar da shi.
“Ya kamata ya nada mai taimaka wa gwamna ta fuskar tsaro domin mutane su san wanda za su kira a lokacin suka samu kansu yayin da aka afka musu, ba mu ma san abin da za mu yi ba a yanzu, ‘yan fashi za su shiga tsakiyar gari su kashe mutane, abin ya tayar da hankali matuka.” Cewar Ishaq.
LEADERSHIP ta rawaito cewa hedikwatar karamar hukumar Bungudu na da tazarar kilomita 21 zuwa babban birnin jihar.
Idan dai ba a manta ba an kashe ‘yan sanda hudu a watan da ya gabata a karamar hukumar, sannan an kashe wani dan sanda a kwanakin baya a wasu hare-hare da aka kai yankin.
Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, sai dai bamu same shi ba, domin bai amsa kiran waya da aka yi masa ba.