Mahimmancin Zaman Lafiya

Wurin Karatu – Romawa 12:1 8: “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwalgwadon iyawarku.” Shalom!
Zaman lafiya abu ne mai mahimanci ga kowane mutum da kuma dukan halitun ubangiji Allah. Zaman lafiya abu ne da kowane mutum ko halite na bukatarsa. Maganan zaman lafiya ta zama wata abu ne dukanmu, mu na sane da cewa doles ne kowa ya kawo nasa ko nata gudumuwa domin a sami cikaken zaman lafiya.
Sakon addinin Kirista ko kuwa bishara da Yesu Almasihu ya kawo ga mutanen duniya shine bisharan salama ko na zman lafiya ga duniya. Zaman lafiya wata abu ne mai yiwuwa ga kowane irin mutum day ay yi niyya.
Zaman lafiya itace tushin rayuwa da kuma cingaba na kowane irin al umman duniya. Zaman lafiya kowane jinsin al umma abu ne mai yiwa domin kyakyawan fihimtan juna. Zaman lafiya yakan inganta kyayawan zamanta kewa lafiya ne akan kyautata mu’amula.
Bisa ga koysuwan addini Kirista, zaman lafiya na yiwuwa ga kowane Kirista na gaskiya. Watau alaman Kiristan gaskiya shine, zaman lafiya da kowane irin mutum. Watau Kiristan gaskiya, wakili ne na zaman lafiya ko na wanzar da zaman lafiya.
Ba a iya raba cikaken Kiristan duniya da zaman lafiya domin it ace cikon addinin Kirista. Allah ubangiji na Magana da cewa: “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane….”Anan ubangiji Allah na nuna mana da cewa, maganan zaman lafiya na yiwuwa, to umurini ne ga Kiristan duniya ya zauna lafiya da kowane Bil Adama komi bambamcin addini ko jinsi.
Zaman lafiya mai yiwuwa ne, matuka kowa da kowa ya kawo nasa gudumuwan zaman lafiya. Zaman lafiya na tabbata ne, in kowa ya bi umurnin Allah akan zaman lafia. Cikaken addini ko saukaken addini na gaskiya, addini ne mai koyas da maganan zaman lafiya ga dukan Bil Adama.
Duk masu bin saukaken addinai, suna. Sane da cewa zaman lafiya haki ne akan mabiya ko masu imani ga Allah. Allah ubangiji ya dorawa kowane Kirista hakin zaman lafiya da kowa a kowane mataki. Duka Kirista na gaskiya na sane da cewa, matuka bai zauna lafiya da kowane irin mutum ba, to ya saba koyswar addini Kirista. Duk Kiristan duniya da ya zauna lafiya da kowane irin mutum, alama ce shi Kirista na gaskiya ne. Zaman lafiya da kowane mutum shaida ne na gaskiya akan Kirista da cewa shi mai bin Yesu Almasihu na gaskiya ne.
Kirista na iya zaman lafiya da kowa, gwalgwado iyawarsu, sai dai in basu yi niyya ba. Watau Allah Ubangiji, ya bai wa Kiristan duniya ikon zaman lafiya tare da itace siffar cikaken addini. Ko kuwa addinin zaman lafiya ana gane da ita wurin alamar wanzar da zaman lafiya tare da kowa.
Abinda ya sa addinin Kirista ya bad mahimanci akan maganan zaman lafiya shine, babu yadda Kirista zai iya bautar Allah ba tare da zaman lafiya ba. Kirista ba zai iya yin ibadarsa har ta zama karbabuwa ga Allah matuka babu zaman lafiya.
Akwai abubuwan da ke hadasa rashin zaman lafiya kama nuna bambancin addini ko kyaman addinin wani, kiyayya, tsanan ta mabambantan addinai, rashin adalci, da ire irensu. Allah ubangji ya yi mana rigakafin rashin zaman lafiya tawurin.
Umurnin day a umurci kowane Kiristan duniya da cewa:
“…ku yi kammar magabtanku, kuma wadanda su kan tsananta maku, ku yi masu addu’a” (Matta 5:44)
Domin tsananin mahinmancin zaman lafiya a cikin addinin Kirista said a Allah ubangiji tawurin Yesu Almasihu ya umurci Kiristan duniya das u kamnar magabansu. Ba zai zama da sauki ba, a ce wai mutum ya kauna ci magabcinsa. Amma wannan umurnin da Allah ya umurci Kiristan duniya day a kaunci masu gaba das u wata hikima ne domin wanzar da zamna lafiya tsakanin magabta. Kauna ga magabci, itace kadai mafita ko karshen kiyeya tsakani Kirista da wanda ba Kirista ba.
Matuka Kirista ya kaunaci wanda ke gaba da shi, wannan itace karshe gaba da juna. Kiristan duniya a kowane lokaci yak an sami nasara akan makiyinsa tawurin kaunar day a kan nunawa magabtansa. Kiristan duniya a tsowon tarihinsa, su kan zama masu nasara akan masu tsananta masu tawurin kaunar magabatarsu da kuma yi masu addu’a.
Garkuwar nasara Kiristan duniya akan magabtarsu da masu tsananta masun a ko ina da kuma a kowane lokaci shine kauna da addu’oi domin magabta da masu tsananta masu.
Watauc asirin nasaran Kiristan duniya akan magabtar su da masu tsananta masu shine kauna da addu’a sune makamin nasaran Kiristan duniya.
Domin da haka hahimanci zaman lafiya na samuwa ne tawurin nunawa magabtarsu kauna da yiwa masu tsananta masu addu’a. Allah ya bamu ikon kaunar magabtarmu a cikin kowane hali kuma ya bamu dama da ikon yiwa masu tsananta mana addu’a domin su sami ceto Allah ta wurin Yesu.
Almasihu mai ceton duniya, amin!
Shalom! Shalom!! Shalom!!!

Exit mobile version