Ranar 14 ga watan Satumba na kowacce shekara ta kasance wata rana ta musamman ga kafatanin al’ummar Masarautar Hadeja, sakamakon a ranar ne da Mai Martaba Sarkin Hadeja Dakta Adamu Abubakar Maje yake cika shekara 20 a kan karagar mulki a matsayin Sarkin Hadeja (a cikin jerin sarakunan Fulani) na 16 a Masarautar.
Mai Martaba Sarkin Hadeja kuma shugaban majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, wadda duk duniya ta yi masa shaida wajen hidimta wa addini da al’ummarsa musamman masu karamin karfi, mata da kananan yara da marayu, ya kasance Sarki Mai ilimin addini da na zamani.
Haka kuma cikin shekara ashirin da Sarkin ya share kan karagar mulkin Masarautar, an sami gwaggwaban ci gaba a fannonin rayuwa a yankin, wadda hakan ya sanya Masarautar ta Hadeja ta zarce sa a akowanne fanni na rayuwa.
Masarautar Hadeja ta kasance daya daga cikin masarautu biyar masu dumbin tarihi a jihar Jigawa da ma kasar Hausa baki daya, haka kuma Sarkin na Hadeja shi ne a matsayin jagora ga dukkanin sauran masarautun da ke fadin jihar.
Yankin na Hadeja wadda ya kunshi manyan garuruwa masu tarihi a kasar Hausa, na da kananan hukumomi guda takwas da suka hada da Hadeja, Kafin Hausa, Auyo, Malam-madori, Kaugama, Kiri-kasamma, Birniwa da karamar hukumar Guri.
Yankin Hadeja wadda ke Gabashin jihar ta Jigawa, Allah ya albarkace shi da masu ilimin addini da na zamani, ga kasar noma da kasuwanci, manyan ma’aikata a matakin kasa da jiha baki daya, wadda hakan ya sanya yankin bunkasa fiye da kowanne yanki a jihar.
Dangane da kafuwar masarautar kuwa, tarihi ya nuna cewa, yankin na Hadeja na da dimbin tarihi tun Kafin zuwan turawan mulkin mallaka domin kuwa ko a wancan lokaci, Hadeja Masarauta ce mai kunshe da Jarumai, Attajirai da Masana illimi.
Tarihi ya bayyana cewa tun kimanin shekarar 11,000, Habe ke mulki a yankin Garun-Gabas wadda ke karkashin karamar hukumar Malam-madori a yanzu, kuma sun yi fitattu kuma jaruman Sarakuna masu yawa wadanda suka hada da Sarki Kankarau, Asawa, Mamman Bako, Kawu, Baude, Musa da Kuma Abubakar.
Haka kuma tarihi ya bayyana cewa, a shekarar 1808 ne Fulani suka fara karbe mulki daga Habe a masarautar ta Hadeja kuma suka ci gaba da yi har zuwa wannan lokaci.
“A Lokacin Sarkin Hadejia na Habe Abubakar ne Fulani suka zo kasar Hadejia, a karkashin jagorancin Ardo Abdure dan Jamdoji, kuma Sarkin Habe Abubakar shi ne ya basu wurin zama, kana a zamanin Sarkin Fulani Sambo suka dawo Inda fadar Hadejia take yanzu, kafin daga bisa su kwaci mulki a hannun Sarakunan Habe a karkashin tutar Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo”.
Sarakunan Fulani a masarautar ta Hadeja sun hada da Sarki Umaru Dan Ardo Abdure 1805 – 1808, Sarki Mamman Kankiya Dan Umaru 1808 – 1808, Sarki Sambo Dan Ardo Abdure 1808 -1845, sai kuma Sarki Garko Gambo Dan Sambo 1845 – 1847, Sarki Abdulkadir Dan Sambo 1847 – 1848, Sarki Sambo Dan Ardo Abdure 1848 – 1848 (Hawa na biyu).
Sai Kuma Sarki Buhari Dan Sambo 1848 – 1850 (hawan farko), Sarki Ahmadu Dan Sambo 1850 – 1851, Sarki Buhari Dan Sambo 1851 – 1863 (Hawa na biyu), Sarki Umaru Dan Buhari 1863 – 1865, Sarki Haruna Bubba Dan Sambo 1865 – 1885, Sarki Muhammadu Maishahada Dan Haru Bubba 1885 – 1906.
Sauran Sarakunan sun hada da Sarki Haru Mai Karamba Dan Muhammadu 1906 – 1909, Sarki Abdulkadir Dan Haru Mai Karamba 1909 – 1925, Sarki Usman Dan Haru Mai Karamba 1925 – 1950, Sarki Haruna Dan Abdulkadir 1950 – 1985, Sarki Abubakar Maje Dan Haruna 1985 – 2002, sai kuma Mai Martaba Sarki Dakta Adamu Dan Abubakar Maje wanda shi ne a kan karagar mulkin Masarautar Hadeja har zuwa yanzu.
Mai martaba Sarki Dakta Adamu Abubakar Maje ya kasance Sarki na 16 a jerin Sarakunan Fulani a Hadeja, kuma ya zama Sarki a ranar 14 ga watan Satumbar shekarar 2002, bayan rasuwar mahaifinsa a ranar 11 ga watan na Satumba.
Kafin rasuwar mahaifinsa ya nada shi a matsayin IYAN HADEJA na farko, a ranar 3 ga watan Janairun shekarar 1999 yadda daga bisani ranar Laraba 11 ga watan Satumba na shekarar 2002 kuma Allah ya yi wa mahaifin nasa rasuwa.
Sannan a ranar 14 ga watan Satumbar kamar yadda al’adar Masarautar ta amince a nada sabon Sarki Kafin kwanaki uku da rasuwar wadda ke karagar. Don haka majalisar Sarki suka nada shi a matsayin sabon Sarkin Hadeja na 16 bayan amincewar gwamnatin wannan lokaci.
Haka kuma an yi bikin bashi Sanda a ranar 29 ga watan Maris 2003, wadda gwamnan jihar Jigawa a wannan lokaci Alhaji Ibrahim Saminu Turaki ya jagoranta kuma aka gudanar a filin wasanni na Hadeja.
Mai Martaba Sarki bayan an bashi Sandar jagorancin kasar Hadejia a karkashin tutar Shehu Usman Dan Fodiyo, yadda daga nan kuma shagulgulan biki suka fara.
Mai Martaba Sarki ya gudanar da kayatattun Hawa guda uku tare da gudanar da addu’o’i da karatun Alkur’ani a Masarautar.
Shi dai Mai Martaba Sarkin Hadeja an haife shi ne ranar 15 ga watan Oktoba na shekar 1960, a cikin birnin Hadejia a tsohuwar Jihar Kano.
Mai Martaba Sarki ya fara karatun firamare a shekar 1967 zuwa 1972 a Makarantar Abdulkadir Primary school Hadeja. Daga bisani ya shiga Makarantar Sakandire ta Garin Ikot Ekpene Cross-riber a shekarar 1973 zuwa1976, sannan ya koma makarantar Sakandire ta Danbatta a shekarar 1976-1979.
Mai Martaba Sarki ya samu nasarar shiga Makarantar Gaba da Secondary ta school of Rural and social science da ke Rano a Jihar Kano a shekarar 1981-1982, da kuma 1983-1985.
Mai Martaba Sarki ya fara aikin Gwamnati a tsohuwar Jihar Kano a ma’aikatar walwalar al’umma, a shekarar 1982-1988, sannan ya koma hukumar jindadi da walwalar Alhazai ta jihar Kano a shekarar 1988-1991.
Bayan da aka kirkiro Jihar Jigawa Mai Martaba Sarkin Hadejia ya koma hukumar jindadi da walwalar Alhazai ta jihar Jigawa a shekarar 1991-1998. Sannan ya koma Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta jiha a shekarar 1998-1999.
A wannan shekarar ne Mai Martaba Sarkin Hadejia Dakta Abubakar Maje Haruna ya nadashi sarautar IYAN HADEJA kuma dan majalissar Sarki kafin daga bisani kuma a nada shi a matsayin Sarkin Hadeja na 16.
Daga karshe jaridar LEADERSHIP Hausa da ma’aikatanta na taya Mai Martaba Sarki murna tare da fatan Allah ya kara wa Sarki lafiya da nisan kwana masu albarka.