Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Gwale, Khalid Ishaq Diso na tsawon watanni uku.
An zargi Diso, dan jam’iyyar APC, da sayar da filayen gwamnati ba tare da neman shawarar kansilolinsa ba.
Majalisar ta dauki matakin ne bayan ta amince da rahoton kwamitinta kan harkokin kananan hukumomi da masarautu a zauren majalisar a ranar Talata.
Majalisar ta ce, kansiloli shida cikin 10 na karamar hukumar sun shigar da kara kan ayyukan shugaban da ba su gamsu da su ba.
Kakakin majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya ce ana kuma zargin shugaban da yanke hukunci ba tare da tuntubar kansilolinsa ba.
Majalisar ta kafa wani kwamitin wucin gadi da zai binciki zarge-zargen tare da bayar da rahoto nan da watanni biyu.
Hakazalika, ta umurci mataimakin shugaban majalisar da ya karbi ragamar mulki har sai an kammala bincike.