• English
  • Business News
Saturday, July 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Ɗinkin Duniya Da Tarayyar Turai Sun Miƙa Cibiyar Kula Da Matan Da Aka Ci Zarafinsu Ga Jihar Sokoto

by Abdulrazaq Yahuza
2 years ago
in Labarai
0
Majalisar Ɗinkin Duniya Da Tarayyar Turai Sun Miƙa Cibiyar Kula Da Matan Da Aka Ci Zarafinsu Ga Jihar Sokoto
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yayin da aka kammala aikin shirin kawo karshen cin zarafin mata na Kungiyar Tarayya Turai (EU) da Majalisar Dinkin Duniya tare da mikawa ga masu ruwa da tsaki, Gwamnan Jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa bisa tallafin shirin, gwamnatin jihar ta inganta kula da wadanda suka tsira daga Cin Zarafi na Jinsi (SGBV) a cikin jihar.

“Mun inganta ayyukan kula da waɗanda suka tsira daga cin zarafi na Jima’i saboda bambancin jinsi (SGBV) kuma mun tabbatar da cewa mata da ‘yan mata sun sami damar samun kulawar da suke buƙata don sake gina rayuwarsu.” Ya bayyana hakan ne a wajen taron kammala shirin tare da mika cibiyar da aka samar ga Gwamnatin Jihar Sokoto, a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, a dakin taro na kasa da kasa da ke Sokoto.

  • Mata A Nemi Sana’a Kuma A Yi Addu’a – Asma’u Kabir
  • Dino Melaye Ya Lashe Akwatin Zabensa A Kogi

Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Alhaji Aliyu Dikko, ya jaddada cewa “jihar ta yi namijin kokari wajen tabbatar da cewa mata da ‘yan mata sun samu kulawar da ta dace, tare da saukaka yunkurin farfadowa don sake gina rayuwarsu bayan da suka tsallaka siradi.

Ya nanata kudurin jihar na kawar da cin zarafi da munanan ayyuka da ake yi wa mata da ‘yan mata, ya kuma jaddada gagarumin ci gaban da aka samu ta hanyar shirin mai lakabin ‘Spotlight Initiative’, wanda ya kasance wani cikakken shiri da aka tsara don tabbatar da cewa kowace mace walau babba ko yarinya za ta iya rayuwa a Jihar Sokoto ba tare da fuskantar wani tashin hankali da abubuwa na cin zarafi ba.

“Gwamnati ta himmatu wajen samar da dokoki da tsare-tsare da za su kare mata da ‘yan mata, tare da samar da yanayin da zai tabbatar da yin hukunci da adalci ga wadanda suka tsira daga cin zarafin mata a Jihar Sakkwato.” Ya bayyana.

Labarai Masu Nasaba

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

Sokoto

Babban jami’in kula da kananan yara na Asusun UNICEF, Ibrahim Sesay, wanda ya wakilci Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron ya ce, “A cikin shekaru biyar da suka gabata, tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Sokoto, shirin na ‘Spotlight Initiative’ ya samu gagarumar nasara wajen magance matsalolin da suka shafi cin zarafin mata (GBV) da sauran munanan dabi’u da miyagu ke aikatawa a kan mata manya da yara.”

Ya bayyana wasu muhimman nasarorin da shirin ya samu kuma da suka hada da: samar da dokar kariya ga yara, da kafa Cibiyar Kula da Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafi (GBV), da yaye sama da mata 9,000 da aka koyar a karkashin shirin ilimi na musamman da aka tsara ga wadanda ba su yi karatu ba.

Sesay ya jaddada yawaitar abubuwan da ba su dace na zamantakewar al’umma da ake yi kamar aurar da ‘ya’ya mata da wuri, da kaciyar mata a Jihar Sakkwato, yayin da a cewarsa, har yanzu Nijeriya na ci gaba da fama da wadannan matsaloli da suka hada da aurar da ‘ya’ya mata kanana su miliyan 26 da wasu miliyan 19.9 da suka sha da kyar sanadin yi musu yankan gishiri.

“Wannan biki na rufewa ya zama kira ga masu ruwa da tsaki da su jajirce wajen ganin sun kare hakkin mata da yara a Jihar Sakkwato. Har ila yau, shirin yana bukatar gwamnati ta ware wani kaso na kudi tare da ba da fifiko ga kare yara da inganta daidaito tsakanin jinsi da karfafa mata.”

Sokoto

Kwamishiniyar kula da harkokin mata da yara na Jihar Sokoto, Hajiya Hadiza Ahmed Shagari ta bayyana cewa kare lafiyar mata da ‘yan mata na da matukar muhimmanci a Jihar Sokoto, don haka ne aka kafa wata cibiya mai suna ‘Nana Kadija Centre’.

Kwamishiniyar wadda babbar sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Aisha Mohammed ta wakilta, ta bayyana cewa, “Mun samu nasara tare da yin aiki tare da dukkan abokan hulda na hukumomi, da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda suka jajirce wajen gudanar da ayyuka daban-daban na magance cin zarafin mata da kuma kare yara a Jihar Sokoto.”

Alkalin Alkalan Jihar Sokoto, Hon. Mai shari’a Muhammad Sifawa, wacce Hajiya Mariya Haruna ta wakilta, ya bayyana jin dadinsa ga hukumar shari’a ta Jihar da kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya bisa goyon bayan da suka bayar tun bayan fara aikin a shekarar 2019.

Ya ce, “Ma’aikatar shari’a ta kuduri aniyar dagewa a kokarinta na ganin an gaggauta gudanar da shari’a kan laifukan da suka shafi cin zarafi na jinsi (GBV) da kuma munanan halaye, don tabbatar wa mata da ‘yan mata cewa akwai wani wuri mai aminci da za su iya kai kokensu duk lokacin da suke buƙatar hakan.”

Shirin na haɗin gwiwar ‘EU da UN Spotlight Initiative’, na da nufin kawar da cin zarafin mata da ‘yan mata da yaki da abubuwa masu cutarwa a Nijeriya, inda ya yi tasiri mai mahimmanci tun lokacin da aka kafa shi a 2019. An aiwatar da shirin cikin nasara a jihohi biyar: Adamawa, Kuros-Riba, Ebonyi, Legas, Sokoto, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AmurkaCin ZarafiKaciyar MataMDDSinSokotoUN
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kasar Sin Na More Ci Gabanta Da Kasashen Afirka

Next Post

Alfanu Da Matsalolin Raba Wa Kishiyoyi Gida

Related

Fyade
Rahotonni

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

2 hours ago
APC
Manyan Labarai

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

3 hours ago
A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya
Labarai

A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Gaban Kotu A Matsayin Lauya

14 hours ago
Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano
Labarai

Biyan ‘Yan Fansho Naira Biliyan 22: NUP Da NLC Sun Bukaci A Yi Koyi Da Gwamna Abba

15 hours ago
Kasar Sin Ta Nuna Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Nijeriya Buhari
Labarai

Za A Dinga Tunawa Da Buhari A Matsayin Waliyyi A Siyasar Nijeriya —Dakta Zangina

16 hours ago
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Manyan Labarai

Tinubu Ya Nada Ɗan Babangida A Matsayin Shugaban Bankin Manoma

17 hours ago
Next Post
Alfanu Da Matsalolin Raba Wa Kishiyoyi Gida

Alfanu Da Matsalolin Raba Wa Kishiyoyi Gida

LABARAI MASU NASABA

Shettima

Nijeriya Za Ta Rika Samun Naira Tiriliyan Uku A Aikin Tatsar Rogo Duk Shekara – Kashim

July 19, 2025
Fyade

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

July 19, 2025
APC

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

July 19, 2025
Dangote

Dalilin Da Ya Sa Dangote Ya Jinjina Wa Hukumar NPA

July 18, 2025
Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin

July 18, 2025
2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC

July 18, 2025
Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

Kasar Sin Ta Gano Ma’adanin Yuraniyom Mafi Daraja A Karkashin Kasa Mai Zurfi

July 18, 2025
majalisar kasa

Kirkirar Sabbin Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Dabaibaye Sauraron Jin Ra’ayoyin Gyaran Tsarin Mulki

July 18, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Zambia Da Ci 5-0

July 18, 2025
Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

Yawan Jarin Waje Da Sin Ta Samu Ya Haura Dalar Amurka Biliyan 700

July 18, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.