A ranar Asabar 18 ga watan Yuni, Majalisar malamai ta yankin jihohin Yarbawa wanda suke da cibiya a Ibadan babban birnin jihar Oyo suka nada gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, Sarautar ALAUDDEN Na YORUBAWA (ALADDIN Na YORUBA).
An yi nadin sarautar ne karkashin Jagorancin Shugaban majalisar limamai da malamai na Jihar Oyo, Sheikh Abdulganiyy Abubakar (AGBOLOMOKEKERE).
- Ganduje Ya Nada Baffa A Matsayin Shugaban Hukumar Kare Hakkin Masu Siye Da SiyarwaÂ
- Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Ganduje Ya Ciyo Bashin Biliyan 10 Don Sayen Na’urar CCTV
Hadimin gwamnan Kan daukar hoto, ya bayyana cewa, Shugaban majalisar malaman ya ce, ana bayar da sarautar ne kadai ga musulmi mai riko da addini da kuma yi wa addinin hidima inda bincikensu ya tabbatar musu da gwamnan Kano Ganduje shi ne ya cika wannan sharudan.
Idan za’a iya tunawa gwamna Ganduje shi ne shugaban gidauniyar addinin musulunci ta Ganduje foundation wacce ta shafe sama da shekaru Ashirin tana hidima ga addini, musamman wajen gina Masallatai, Makarantu, Asibitoci, aikin gina rijiyoyin burtsatse, musluntar da maguzawa da sauran su.