ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Wakilai Ta Nemi A Cefanar Da Sufurin Jirgin Kasa

by Bello Hamza
2 years ago
Jirgin Kasa

Majalisar wakilai ta nemi gwamnatin tarayya ta yi gwanjon harkokin tafiyar tare da gudanar da hukumar jirgin kasan Nijeriya (NRC).

Kiran ya biyo bayan amincewa da kudurin da Dan Majalsia Sada Soli Jibia mai wakiltar mazabar Jibiya a jam’iyyar APC ta jihar Katsina, a zaman majalisar ranar Alhami na makon jiha.

  • Yadda Rakiyar Gwamnan Kano Ga Tagwayen da ke Manne Da Juna Ta Dauki Hankalin Al’umma
  • Mutum Miliyan 2 Za Su Ci Gajiyar Tallafin Kiwon Lafiya A Bauchi

Da yake gabatar da kudurin, ya bayyana cewa, “Bangaren harkokin jiragen kasar Nijeriya na samar da ayyukan yi ga dimbin matasa yana kuma taimaka bunkasar tattalin arzikin kasa.”

ADVERTISEMENT

Ya ce, duk da dimbin jari da ake zubawa a bangaren, ayyukan hukumar jiragen kasa sai kara tabarbarewa yake yi, musamman in aka kwatantasu da takwarorinsu na sauran bangaren tattalin arzikin kasa.

Ya kuma yi korafin cewa, gwamnatocin da suka gabata sun kasa samar da hukumar jiragen kasa mai inganci da Nijeriya za ta yi alfahari da ita.

LABARAI MASU NASABA

Danyen Mai Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.436 —OPEC

An Jinjina Wa Tinubu Bisa Mayar Da Ofishin Ayyukan NPA Garin Warri

Dan majalisar ya kuma ce, rashin ci gaba a harkokin jiragen kasan Nijeriya ya taimaka wajen tabarbarewa hanyoyin kasar nan wanda hakan yake jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma a kullun garin Allah ya waye.

A kan haka ya nemi ta gaggauta sayar da dukkan harkokin gudanarwar jiragen kasan Nijeriya ga ‘yan kasuwan da kamfanoni masu zaman kansu, kuma al’umma da dama a kasar nan sun amince da yin haka.

Ya kuma lura da cewa, sayar da harkokin tafiyar da jiragen kasa abu ne da ya karbu a sassan duniya, musamman ganin yin haka zai kai ga samar da tsaftaccen harkar jiragen kasa zai kuma samar da ayyukan yi ga matasa zai kuma rage cin hanci da rashawa.

A kan haka majalisar ta umarci gwamnatin tarayya ta hada hannu da kwamitin majalisar a kan hakokin sufuri su don shirya yadda za a cimma wannan burin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Danyen Mai Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.436 —OPEC
Tattalin Arziki

Danyen Mai Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.436 —OPEC

December 19, 2025
An Jinjina Wa Tinubu Bisa Mayar Da Ofishin Ayyukan NPA Garin Warri
Tattalin Arziki

An Jinjina Wa Tinubu Bisa Mayar Da Ofishin Ayyukan NPA Garin Warri

December 19, 2025
Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
Tattalin Arziki

Gwamna Radda Ya Dora Harsashin Gina Ma’aikatar Sarrafa Rogo A Katsina

December 13, 2025
Next Post
Gwamna Lawal Ya Ziyarci Hukumar ‘Yan Gudun Hijira, Ya Karbo Wa Zamfara Kayan Tallafi

Gwamna Lawal Ya Ziyarci Hukumar 'Yan Gudun Hijira, Ya Karbo Wa Zamfara Kayan Tallafi

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.