Adadin makafi 37 ne suka rubuta jarabawar UTME ta shekarar 2025 a cibiyar zana jarabawar JAMB ta musamman da ke Bauchi, wadda ta gudana a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) reshen Yelwa. Wannan shirin na daga cikin Æ™oÆ™arin gwamnati na bayar da dama ga masu buÆ™ata ta musamman don su samu ilimi da kuma damar shiga manyan makarantu.
Farfesa Hadiza Isah Bazza, mataimakiyar jami’in kula da cibiyar, ta bayyana cewa É—aliban sun fito daga jihohin Bauchi, da Borno, da Gombe da Yobe, kuma shirin JAMB na musamman ga naÆ™asassu ya fara ne tun daga shekarar 2017.

Tuni shugaban JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya ba wa shirin muhimmanci
wanda ke bai wa naƙasassu damar zana jarabawar ba tare da wani tangarɗa ba.
Gwamnatin tarayya ta É—auki nauyin dukkanin buÆ™atun É—aliban na zana jarabawar, ciki har da abinci da wurin kwana, har na tsawon kwanaki uku. Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dakta Lawal Mohammed Rimin Zayam, ya yaba da wannan mataki na JAMB, yana mai kira ga iyaye da su tura ‘ya’yansu dake da lalura ta musamman makaranta domin samun ilimi.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’umma da iyaye su fahimci muhimmancin ilimi, musamman ga yara masu naÆ™asa, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da wayar da kan iyaye don ganin suna tura ‘ya’yansu makaranta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp