A makon da ya gabata ne makarantar Imam Sagir dantaura da ke karamar hukumar Ungoggo Gayawa da ke Jihar Kano ta yi saukar karatun na kimanin goma sha biyar.
A wannan makaranta mai suna Imam Sagir dantaura wannan sauka ba itace ta farko ba. A’a wannan shi ne karo na uku hakane ma wannan guri ya sami halartar manya baki da dama irinsu kwamandan Hisba da As As da As ta mata Malama Bahijja Rano da jagoran siyasar Ungoggo Malam Abdullahi Bagobiri sai tsohon ciyaman kuma As na gwamna shehu Aliyu Ungoggo.
Sai Wakilin dan majalisar tarayya wato Mai Wake. Sai uban makarantar shi Imamin masallacin Murtala liman Kabiru Badamasi dantaura. Da ma wasu da dama da su ka zo wannan saukar bayan tashi sakataran wakilinmu ya sami ganawa da shi shugaban makarantar Imam Sagir dantauran ya yi karin haske ga me da makasudin shirya wannan sauka da kuma gayyatar wannan mutane ya ce wannan makaranta ta yaye dalibai goma sha biyar kuma abin mamaki shi ne. A duk sha biyar din nan na ji daya ne wannan abin shi kansa wakilin gwamna wato kwamandan Hisba sai da ya jinjina wannan.
Ya ce samun kokarin mata a duk rayuwa gaskiya sun fi maza domin da yawa yaranmu sai wasa kawai suka sa a gaba amma muna fatan zasu gyara domin wannan ya zame musu darasi.
Kuma karatun nan yinsa muke yi domin ba wannan ne karon farko ba da muka yaye dalibai ba a wannan makaranta a’a wannan shi ne karo na uku amma abin da yake damun mu shine kulawar iyayen mu ta gefe guda muna yin abin da ya kamata amma akwai hakkoki da ya kamata su iyaye su dinga bawa yara suna kawo mana. Domin wannan taimakon shine dai wanda muka dogara da shi domin ita makaranta babu inda zata sami taimako sai ta wannan hanyar kirana ga iyaye su kula da wannan hakkin domin da wannan ake sallamar Malamai dan Allah a dinga kulawa.
Ya ce, wannan makaranta ta na godiya ga duk iyaye da hadin kan da suke basu ya kara da cewa yana godewa malaman da su ke bada gudunmawa a wannan makaranta ya ce dama matsalolin wannan makaranta shi ne karancin aji mu na da dalibai kusan dubu da dari biyar amma ajin da mu ke karatu uku ne kawai ka ga wannan ai babbar matsalace to babban kalubalanmu shi ne zuwan da mu na ko sanyi dole mu ke tashin yaran saboda sanyi ko damuna amma zuwan kwamandan Hisba ya yi mana albishir da alkawarin Mai Girma Gwamna cewa duk abin mu ke so to mu rubuta muna mika godiyarmu gare shi kuma kofarmu a bude take kamar mataimakin gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna dama ya saba bada gudunmawa ga al’umma dama duk masu bada taimako muna jira.