Mataimaki na musamman na Gwamnan Jihar Borno a harkokin yada labarai Mallam Isa Gusau ya rasu.
Marigayin kwararren Dan jarida ne, ya rasu da yammacin ranar Alhamis a birnin Landan, inda yake jinyar rashin lafiya.
- Zulum Ya Bayar Da Umarni A Binciki Gawar ‘Yar Dan Majalisa Da Aka Kashe A Jihar Borno
- Cire Tallafin Fetur: Zulum Ya Amince Da Ba Ma’aikatan Jihar Borno Rancen Naira Biliyan 2
Gusau ya fara aiki a matsayin mai taimaka wa gwamna a kafafen yada labarai a Jihar Borno tun lokacin, Sanata Kashim Shettima, yana gwamnan jihar wanda a yanzu shi ne Mataimakin Shugaban Nijeriya.
Bayan wa’adin Gwamna Shettima ya kare, a zangon farkon na Gwamna mai ci Babagana Umara Zulum ya sake nada shi a shekarar 2019, inda ya rike mukamin har zuwa rasuwarsa a ranar Alhamis.
Marigayin tsohon ma’aikaci ne da ya taba aiki da Jaridar Daily Trust a jihar Borno kafin a nada shi mataimakin tsohon Gwamna Shettima a fannin yada labarai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp