• English
  • Business News
Tuesday, May 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Malama Duan Yiruo: Yadda Ake Taimakawa Matasan Afirka Wajen Fahimtar Al’adun Kasar Sin

by Safiyah Ma
1 year ago
in Babban Bango
0
Malama Duan Yiruo: Yadda Ake Taimakawa Matasan Afirka Wajen Fahimtar Al’adun Kasar Sin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sanin kowa ne cewa, kwalejojin Confucius dake kasashen Afirka, suna taka muhimmiyar rawa wajen inganta mu’amalar al’adu, da koyon harshen Sinanci tsakanin Sin da kasashen Afirka. Wata malamar kasar Sin dake koyar da Sinanci ga daliban ketare Duan Yiruo, ta taba aiki a wasu kasashen Afirka uku, wato Kamaru, da Mozambique da Rwanda, kuma a halin yanzu tana aiki a matsayin malamar kasar Sin a kwalejin Confucius dake jami’ar Rwanda.

Ta hanyar aiki a kasashen Afirka na tsawon shekaru da yawa, Duan Yiruo da abokan aikinta sun bude wata sabuwar taga ga jama’ar kasashen Afirka, ta lura da duniya mai launuka, da fahimta, da kaunar al’adun kasar Sin ta hanyar koya musu Sinanci.

  • Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Fara Da Kafar Dama A Farkon Bana
  • Sin Ta Nuna Rashin Gamsuwa Da Barazanar Da Amurka Ta Yi Na Kara Haraji Kan Karafa Da Gorar Ruwa Dake Shiga Kasar Daga Kasar Sin

A watan Fabrairun shekara ta 2012, Duan Yiruo ta sauka a nahiyar Afirka a karo na farko, a matsayin wata malamar koyar da harshen Sinanci mai aikin sa kai, tana koyarwa a kwalejin Confucius ta jami’ar Yaounde ta biyu dake kasar Kamaru. Duan Yiruo ta ce, duk da cewa ta samu cikakken horo kafin ta fara aiki, kuma ta yi shirye-shirye daban-daban kafin ta tafi, amma duk da haka ta fuskanci kalubaloli da dama a fannonin rayuwa da aiki a lokacin da ta isa Afirka.

Duan Yiruo ta ce, “Abu mafi mahimmanci shi ne aikin koyarwa, yawancin dalibai suna magana da harshen Faransanci, don haka ya kamata in koyi wasu kalmomin koyarwa na Faransanci na yau da kullum da wurwuri. A wancan lokacin, sadarwar Intanet ba ta da karfi sosai a Kamaru, saboda haka, tana da wuyar duba wasu bayanan koyarwa ta yanar gizo, shi ya sa muka dogara ga littattafan takarda da wasu faifan CD da aka kawo daga Sin.”

A kwalejin Confucius dake jami’ar Yaounde ta biyu a kasar Kamaru, ana gudanar da harkokin koyar da Sinanci iri-iri, kuma daliban sun kara nuna sha’awa ga harshen, sun kuma kara fahimtar kasar Sin, kuma Duan Yiruo ta karu sosai daga aikin koyarwa, inda ta ce:

Labarai Masu Nasaba

Kauyuka Suna Kokarin Neman Cimma Burin Samun Wadata Tare A Kasar Sin

Ziyarar Xi Jinping A Turai Ta Fitar Da Muryar Kiyaye Zaman Lafiya Da Yin Hadin Gwiwa

“A duk lokacin da na ga suna yin rubutu mai yawa da tsabta a cikin littattafan rubutu, ina yaba musu kwarai, kuma bisa irin wannan jajircewa da suka yi, da yawa daga cikinsu sun karu sosai, har sun zama kwararrun malaman koyar da harshen Sinanci a cikin gida, sun kuma sa ‘yan Afirka da dama sha’awar Sinanci a cikin garuruwansu.”

A watan Janairun shekara ta 2016, Duan Yiruo ta sake zuwa Afirka, inda ta isa kasar Mozambique mai kyan gani. A wannan karon, tana koyarwa a kwalejin Confucius dake jami’ar Mondlane a matsayin malama da gwamnati ke daukar nauyinta, kuma za a iya cewa nauyin da ke wuyanta ya karu sosai. A matsayinta na shugabar fannin karatun harshen Sinanci na farko, kana malamar koyar da Sinanci a jami’ar, da isarta jami’ar, Duan ta fara aiki ba tare da nuna kasala ba, inda ta ce:

“Akwai dalibai sama da 30 a ajin karatun harshen Sinanci, wadanda aka zaba daga cikin dalibai sama da 200 wadanda ke son karatun harshen, ciki har da wani wanda ya zo daga wani wuri mai nisan kilomita fiye da dubu 2 daga babban birnin Mozambique, wato Maputo. A karon farko, na koya musu cin abinci da tsinke, wato Kuai Zi, da rubuta kalmomin Sinanci da alkalamin gashi, da koya musu karanta wakoki cikin Sinanci, na kuma ga sun dauki makirufo don gabatar da wani shiri cikin harshen Sinanci a karon farko, na kuma yi amfani da kyamarata don nadar hakan, kuma sun burge ni sosai.”

Duan Yiruo ta kara da cewa, daliban kasar Mozambique sun fara koyon Pinyin, wato yadda ake furta harshen Sinanci ta haruffan Turanci, al’amarin da ya sa suka karu da harshen a sannu a hankali, wadanda suka burge ta kwarai da gaske, inda ta ce:

“Abin da ya fi ba ni sha’awa shi ne dalibai biyu a aji na farko, daya daga cikinsu sunansa Wang Hao a harshen Sinanci, yana da kuzari sosai, yana sha’awar rawa da rubuta wakoki, kuma wani lokaci ma ana gayyatarsa zuwa gidan talabijin don daukar shirye-shirye. Bayan da ya koyi harshen Sinanci na wata uku, ya mayar da abin dake cikin littafin zuwa wakokin rap, wannan hanyar koyon Sinanci ta baiwa dukkan malamai mamaki. Bayan da ya koyi Sinanci na tsawon shekara daya da rabi, ya cimma burinsa na zuwa kasar Sin don ci gaba da karatu. Ina masa fatan alheri a fannin kara karatun harshen Sinanci.”

A watan Yulin shekarar 2023, Duan Yiruo ta fara aikin koyarwa a kwalejin Confucius dake jami’ar Rwanda. A ra’ayinta, a matsayin wata malamar koyar da Sinanci, ba ma kawai tana bukatar gabatar da kyawawan al’adun gargajiyar Sin zuwa ga daliban kasar Rwanda ba, har ma da gabatar da salon zamanin kasar Sin, musamman aiki, da nazari, da rayuwar matasan kasar na wannan zamani, domin su kara fahimtar juna, ta yadda za su yi sha’awar koyon Sinanci, da himmatuwa don kara koyon al’adun Sinawa. Duan ta ce:

“Za mu yi bayanin manyan abubuwan kirkire-kirkire guda hudu na kasar Sin a lokacin karatu, sannan kuma zan kara sabbin manyan abubuwan kirkire-kirkire guda hudu na kasar Sin na wannan zamani, kamar su biyan kudi ta wayar salula, sayayya ta yanar gizo, da sauransu. Dalibai suna sha’awar wasu abubuwa a kasar Sin na zamani. Suna samun natsuwa a cikin aji.”

Duan Yiruo ta ce, yanzu haka kamfanoni da dama na kasar Sin sun zo kasar Rwanda, don zuba jari da gina masana’antu, wanda hakan ya samar da guraben aikin yi ga jama’ar kasar, kuma wasu daga cikin dalibanta sun ci gajiyar koyon Sinanci, daliban suna godiya sosai ga tallafi da goyon bayanta. Ta ce,

“Yanzu Sinawa da yawa suna zuba jari a nan, kuma dalibaina sun samu wasu guraben ayyukan yi kamar aikin fassara. Ni ma ina alfahari da hakan. A karshen zangon karatu da ya gabata, dalibaina sun ba ni wata jakar littafi, wanda hakan ya burge ni kwarai. A gani na bayan na dawo kasar Sin, idan na kalli wannan kyauta, zan rika tunawa da lokacin da na yi aiki a nan.”

Ye Xing, wani dalibi ne dake koyon ilmi dake jami’ar Rwanda a aji na uku, yana da shekaru 25 a wannan shekara. Ye Xing ya bayyana cewa, malaman Sinawa na kwalejin Confucius suna aiki tukuru, sun kware wajen gabatar da al’adun kasar Sin ta hanyar da matasa ke son ji da gani, kuma sun kulla abota mai zurfi da daliban.

Ya kara da cewa, malama Duan ta taba ba su shawarar wasu kyawawan masu rubutun ra’ayin yanar gizo, kuma za su iya koyon al’adun Sinawa daga wadannan bidiyoyin. Ban da hakan, ta kuma gabatar da shirye-shiryen talabijin da yawa ga dalibai, inda dalibai za su fahimci hanyoyin sada zumunta, da nishadantarwa na matasan kasar Sin, wanda hakan zai taimaka masa matuka wajen yin karatu a kasar Sin a nan gaba.

Baya ga Duan Yiruo, akwai malaman kasar Sin da dama dake koyarwa a kwalejin Confucius a kasashen Afirka. Yang Haixia, wata malama ce a kwalejin Confucius a jami’ar Rwanda. Bayan da Yang Haixia ta zo kasar Rwanda, ta gano cewa yanayin rayuwa da aiki a nan na da matukar wahala, amma wadannan matsaloli sun sa ta kara sha’awar aiki da kuma dagewa wajen yin aikin mu’amalar al’adu. Ta bayyana cewa,

“A bangare daya, yanayin rayuwa yana da wahala, a dayan bangare kuma yanayin koyarwa na da matukar wahala. Allunan da aka fi amfani da su ne kawai ke cikin ajujuwa, kuma da karfe aka gina dakunan ajujuwa, da zarar an yi ruwan sama, hayaniyar saukar ruwan sama a kan karfe na sanya ba a iya jin wani sauti na daban. Amma duk da haka, dalibai su kan tambaye ni game da Sin a lokacin karatu da bayan karatu. A duk lokacin da na yi tunanin cewa na horar da kwararru wadanda ke da amfani ga ci gaban al’ummar gida ta hanyar koya musu Sinanci, sai in ji gamsuwa a matsayin wata malama.”

A watan Yulin shekarar 2023, wani malamin Sin mai suna Ming Xing,  ya tafi kasar waje a karon farko, ya fara aikin kula da rajista, koyarwa da sauran ayyuka a lardin Gabashin kasar Rwanda. Ya kan yi amfani da hanyoyi daban-daban don tada sha’awar dalibai don koyo. Dangane da hakan, ya ce,

“Alal misali, ina aika musu da wasu bidiyoyi don koyon Sinanci, ko koya musu wasu wakoki, kuma zan ba su wasu kananan kyautuka a wasu lokuta a kowane mako. A ganina, game da koyarwa, bai kamata a dauke shi a matsayin aiki kadai ba, na dauke shi a matsayin wani nauyi ne da ya rataya a kan wuyana. Wasu dalibai suna son su canza makomarsu ta hanyar koyon Sinanci, shi ya sa ina bukatar kara sha’awarsu wajen koyon ilmin, da kuma koya musu wasu hanyoyin koyon Sinanci.”

Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU ta ayyana shekarar 2024 a matsayin shekara ta ilimi, don inganta sauyin zamantakewar tattalin arziki, da kyautata jin dadin jama’a, da tabbatar da hangen nesa na ajandar 2063. A cikin ‘yan shekarun nan, a karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na kara zurfi a fannin horar da kwararru, kuma hanyoyi da fannoni na hadin gwiwa na ci gaba da habaka. Tun daga gina makarantu da ba da gudummawar kayayyakin aiki, da samar da kwararrun masu ilimin sana’o’i, da tsara horo a fannoni daban-daban, da bunkasa ayyukan gina manyan ayyukan hadin gwiwar horar da kwararru kamar gina kwalejin Confucius, Sin tana ba da taimako sosai ga kasashen Afirka wajen horar da kwararru da suka dace da bukatun zamanintarwa a wurin, ta yadda za a ba da gudummawa wajen inganta ci gaban nahiyar Afirka mai dorewa. A nan gaba, Sin da Afirka za su yi aiki tare don inganta hadin gwiwa a fannoni daban-daban, kuma ana sa ran Sin da Afirka za su samu karin sakamako a karkashin shirin hadin gwiwa na raya kwararru na Sin da Afirka da sauran tsare-tsare.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Harin Ramuwar Gayyar Iran: Isra’ila Na Cikin Tsaka Mai Wuya

Next Post

Hajjin Bana: Jihar Filato Ta Ba Da Kyautar Kujera 500 Da Tallafin Miliyan 2 Ga Duk Maniyyaci

Related

Kauyuka Suna Kokarin Neman Cimma Burin Samun Wadata Tare A Kasar Sin
Babban Bango

Kauyuka Suna Kokarin Neman Cimma Burin Samun Wadata Tare A Kasar Sin

4 months ago
Ziyarar Xi Jinping A Turai Ta Fitar Da Muryar Kiyaye Zaman Lafiya Da Yin Hadin Gwiwa
Babban Bango

Ziyarar Xi Jinping A Turai Ta Fitar Da Muryar Kiyaye Zaman Lafiya Da Yin Hadin Gwiwa

12 months ago
Motocin Sabbin Makamashi Kirar Kasar Sin Sun Mamaye Duniyar Motoci
Babban Bango

Motocin Sabbin Makamashi Kirar Kasar Sin Sun Mamaye Duniyar Motoci

1 year ago
Yadda Nuryan Maimaiti Ke Bayyana Labarai Kan Kogunan Dubban Buddha Na Kezil
Babban Bango

Yadda Nuryan Maimaiti Ke Bayyana Labarai Kan Kogunan Dubban Buddha Na Kezil

1 year ago
Matsayar Sin Game Da Burin Wanzar Da Zaman Lafiya A Duniya
Babban Bango

Matsayar Sin Game Da Burin Wanzar Da Zaman Lafiya A Duniya

1 year ago
Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Ta 2024: Maraba Da Shekarar Kwazo, Kuzari Da Nasara
Babban Bango

Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Ta 2024: Maraba Da Shekarar Kwazo, Kuzari Da Nasara

1 year ago
Next Post
Hajjin Bana: Jihar Filato Ta Ba Da Kyautar Kujera 500 Da Tallafin Miliyan 2 Ga Duk Maniyyaci

Hajjin Bana: Jihar Filato Ta Ba Da Kyautar Kujera 500 Da Tallafin Miliyan 2 Ga Duk Maniyyaci

LABARAI MASU NASABA

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

May 13, 2025
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

May 13, 2025
Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

May 13, 2025
Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

May 13, 2025
Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

May 13, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

May 13, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

May 13, 2025
An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

May 13, 2025
Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.