Bincike ya nuna cewa, duk da tsadar kayan aikin noman rani a bana, da manoman shinkfa da na alkama ke fuskanata a jihar Taraba, sun nuna cewa za su samu amfani mai yawa a bana.
Manoman a fadin jihar, sun bayyana cewa, suna sa ran samun amfani mai yawa na wadannan amfanin nan da mako mai zuwa.
Za a fara diban amfanin gonar biyu ne nan da mako biyu a kananan hukumomi Karim-Lamido da Gassol da Lau da Donga, inda za a yankin Shika, fiye da manoma 200 da suka shuka shinkafa sun fara yankanta.
Rahotannin sun nuna cewa, kashi 60 daga cikin dari na gonakin da aka shuka wadannan amfanin biyu, sun kai munzalin fara dibansu, inda moman na ke da yakinin samun amfani mai dimbin yawa, duk da cewa, sun samu kalubalen dizil da man fetur da suke zuba wa a cikin ijinan ban- ruwansu.
Daya daga cikin manoman ranin mai suna Injiya Yahaya Mafindi, ya bayyana cewa, gonarsa ta shinkfa ta fada cikin ambaliyar ruwan a shekarar da ta wuce, saboda haka ta lalatace, hakan ya sa ya fara yin noman rani da wuri a bana, inda ya ce, nan da mako uku yake sa ran yanke shinkafarsa.
Kashi 60 daga cikin dari na gonakin da aka shuka wadannan amfanin biyu, sun kai munzalin a fara dibansu, inda manoman, ke da yakinin samun amfani mai yawa, duk da cewa, sun samu kalubalen dizil da man fetur da muke zuba wa a cikin ijinan ban-ruwa.
Mafindi ya ci gaba da cewa, da farko ya samu rashin kwarin gwiwa da zai fara yin noman na rani, saboda tsadar man fetur da zai zuba a cikin injin ban-ruwa da zai yi amfani da shi a gonarsa.
A cewarsa, yana da injinan ban-ruwa guda uku da yake yin amfani da su don yin ban-ruwa a gonarsa, amma saboda tsadar man fetur, hakan ya sa ya sayo injinan ban-ruwa mai aiki da hasken rana, inda ya shawarci manoman kar su fara tunin yin noman rani a bana idan sun san ba su da isasun kudin da za su sayi man fetur da iri da magungunna feshi da sauransu.
Shi ma wani manoman na rani mai suna Yakubu Dauda, ya bayyana cewa, kashi 50 daga cikin dari na noman rani da ya yi, ya karbo rancen naira 500, 000 a bana, inda ya kara da cewa, yana sa ran samun shinkafar mai yawa.
Sannan kuma, ya nuna jin dadinsa kan rashin kwarin da ke lalata shinkafar da aka shuka sabanin yadda ta auku a shekarar da ta wuce, musamman a karamar hukumar Lau da Karim-Lamido da Gassol, inda ya kara da cewa, kalubalen da manoman suka fuskanta a wannan shekarar shi ne kawai na tsadar man dizill da na man feutur da suke zuba wa injinan ban-ruwa.
Wani manomin shi ma mai suna Alhaji Isa Tafida, wanda yake bai wa manoman rani rancen kudin yin noman na rani a lokacin aikin shinkafa, ya bayyana cewa, yana bayar da rancen ne kashi 50 a cikin dari, musamman ga manoman da suka yi asara saboda ambaliyar ruwan da ta auku a shekarar da ta wuce a yankin, don su sake farafado wa.
Ya kuma ci gaba da cewa, da alaumun manoman na rani a yankin, bana za su samu amfani mai dimbin yawa, inda ya nuna jin dadinsa kan yadda mnoman za su sake fafrfado wa biyo bayan aukuwar ambaliyar ruwan.
“Na bayar da rancen ne kashi 50 daga cikin dari, musamman ga manoman da suka yi asara saboda ambaliyar ruwan da ta auku a shekarar da ta wuce a yankin, musamman don su sake farafadowa.”
A yankunan Tau da kuma Didango da ke a kananan hukumomin Ardo-Kola da Karim-Lamido akasarin manoman na shinkafar da alkamar da aka tattauan da su sun bayyana cewa, suna sa ran samun amfani mai dimbin yawa.
Daya daga cikinsu, mai suna, Musa Didango ya bayyana cewa, koda yake sun samu kalubalen tsadar kayan aikin na yin noman rani, amma mun ji dadi sosai saboda wa su kalubalen da suka samu na kwarin da ke lalata amfanin gona da kuma na makiyayan da ke tura dabbobinsu cikin gonakinsu.
“Mun ji dadi sosai saboda ba mu fuskanci kalubalen kwarin da ke lalata amfanin gona ba da kuma na makiyayan da ke tura dabbobinsu cikin gonakinmu ba.”