Daraktan ofishin lura da harkokin wajen na kwamitin kolin JKS Wang Yi, da mashawarcin gwamnatin Amurka game da tsaron kasa Jake Sullivan, sun yi tattaunawa mai zurfi da gamsarwa, game da alakar kasashensu a ranar Laraba da jiya Alhamis.
Sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi game da matakan da ya kamata a dauka na kawar da kalubalen da alakar kasashen biyu ke fuskanta, da ma hanyoyin dakile kara tabarbarewar dangantakarsu.
Yayin zantawar Wang, wanda kuma memba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, ya jaddada cikakkiyar matsayar kasar Sin game da batun yankin Taiwan.
Kazalika sassan 2 sun yi musayar ra’ayi game da halin da ake ciki a yankin Asiya da tekun Fasifik, da batun rikicin Ukraine, da sauran batutuwan kasa da kasa da na shiyyoyi dake jan hankalinsu.
Bugu da kari, sassan biyu sun amince su ci gaba da amfani da wannan dama ta tattaunawa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp